✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan takara mai iyali 12 ya samu kuri’a daya a zabe

Zaben ya zama abin magana a kafafen yada labarai na duniya.

Wani dan asalin Jihar Gujarat a kasar Indiya mai suna Santosh Halpati wanda ya tsaya takara a kauyensa a zaben Kananan Hukumomi da aka gudanar a watan jiya ya bar abin tarihi.

Zaben ya zama abin magana a kafafen yada labarai na duniya saboda yadda ya samu kuri’a daya kacal duk da cewa yana da akalla mutum 12 da suka cancanci kada kuri’a a gidansa.

Santosh ya tsaya takarar neman
shugabancin kauyensa (Sarpanch ) a
kauyen Chharwala na Gundumar Vapi,
kuma duk da ba sa ran samun nasara ba, amma bai yi tsammanin samun kuri’a daya kacal ba.

Dan takarar mai matsakaicin shekaru ya yi mamaki lokacin da ake kirga kuri’u a mazabarsa aka ce kuri’a daya da ya jefa wa kansa kawai ya samu, inda ya shaida wa manema labarai cewa yana da ’yan uwa na kut-da-kut 12 da suka cancanci kada kuri’a, don haka ko dai ba su damu da jefa kuri’a ba ko kuma sun zabi wani daban.

“Zabe yana zuwa ya tafi,” inji Santosh kamar majiyar Times Now ta ruwaito.

“Amma na samu kuri’a daya kawai.. ko iyalina ba su zabe ni ba a wannan takarar.”

Irin wannan lamari ya faru shekarun da suka gabata, lokacin da wani dan takara ma zaman kansa daga Jihar Punjab a Indiya ya fashe da kuka yayin da yake shaida wa wani dan jarida cewa, kuri’u biyar kawai ya samu duk da cewa yana da ’yan uwa tara da suka cancanci kada masa kuri’a.

Al’amarin Santosh ya ma fi zafi, domin
bai samu kuri’a daya ba daga wurin
iyalansa sai tasa da ya jefa, kodayake ya ce, mutane da dama sun tabbatar masa da kuri’unsu.