✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

darikar Tijjaniyya a Nijeriya za ta kafa kafar yada labarai

Nan ba da jimawa ba darikar Tijjaniyya a Najeriya za ta kafa wata  kafar yada labarai mai zaman kanta da za ta rika yada manufofinta…

Assheikh Sama’ila Baba Katsina-AlaNan ba da jimawa ba darikar Tijjaniyya a Najeriya za ta kafa wata  kafar yada labarai mai zaman kanta da za ta rika yada manufofinta da kuma kare martabar Musulunci da musulmi.
Assheikh Sama’ila Baba Katsina-Ala, sakataren majalisar malamai na kasa na kungiyar Fityanul Islam ne ya fadi haka a yayin hira da Aminiya, a yayin wata ziyarar da ya kai wa mabiya darikar  ta Tijjaniyya mazauna Kuros Riba a Kalaba, kwanan baya. Ya ce yin hakan ya biyo bayan la’akari da aka yi da yadda Musulunci da musulmi, a kasashen nahiyar Afirka, ke  shan tsangwama da kuma irin yadda wasu ke fakewa da sunan addinin suke ta tabka ta’asa wai suna kishin Musulunci a kasashe daban-daban na nahiyar.
Malamin ya kara da nuna takaicinsa na yadda kafafen yada labarai na Turawan Yamma, a kodayaushe, suke ta watsa labarai na batanci ga Musulunci da musulmi  a duniya.
 “Kodayake yanzu a Nijeriya an fara samun kafar watsa labarai da ke kare martabar addinin Musulunci, shi ya sa mu ma a Tijjaniyya muke son kafa tamu domin kare martabar darikarmu kan batanci da ake yi mata daga mahassadanta”. Inji shi.
Assheikh Baba ya ce ya ziyarci Kuros Riba  ne domin share fagen zuwan shugabannnin darikar na kasa a Nijeriya da kuma a kara karfafa ta a jihar da ma sauran sassan Kudu maso Kudu.
Ya hori mabiyan su kasance, a kodayaushe, masu kankan da kansu, masu son zama lafiya da kowane musulmi, kuma su yi zaman hakuri da kauda kai tsakaninsu da abokan zamansu.
A sakonsa na fatan alheri, wanda Malam Ahmed Sarki Lawal ya karanta, sarkin Hausawan Kalaba, Alhaji Salisu Abba Lawal ya bayyana farin cikinsa da ziyarar malamin tare da fatan ya kasance cikin koshin lafiya a duk inda yake da nufin ziyarta.