✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dattawan APC sun bukaci Buhari ya duba lamarin Babachir

Dattawan jam’iyyar APC na Jahar Adamawa sun roki Shugaba Muhammadu Buhari da ya yi duba bisa al’amarin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Dabid Lawan Babachir wadda aka…

Dattawan jam’iyyar APC na Jahar Adamawa sun roki Shugaba Muhammadu Buhari da ya yi duba bisa al’amarin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Dabid Lawan Babachir wadda aka dakatar da shi daga aiki.

Sun bayyana hakan ne a wani taro da suka yi a Jahar Adamawa, inda suka ce ba a sami Babachir da laifin komai ba, sannan suka bukaci da a mayar da shi bakin aikinsa domin yin adalci a gare shi.

“Muna rokon Shugaba Buhari da ya saki rahotanni da aka yi akan abin da ya janyo dakatar da Babachir domin yin bincike a cikin lamarin in har ba a kama shi da komai ba sai a mayar da shi bakin aikinsa domin kamanta adalci,” in ji su.

Wani tsohon sanata daga Adamawa, Silas Jonathan Zwingina ya ce, APC na jahar Adamawa ta bada goyon bayanta domin shugaba Muhammadu Buhari ya cigaba da mulki a 2019.

Ya bayyana cewa akwai ababe da dama da ya sanya zasu sake marawa Buhari baya a 2019 wadda suka kunshi, kurmushe Boko Haram da tsara hanyoyi a bangarori daban-daban a kasa da inganta noma a kasar da dai sauransu.

Shugaban jam’iyyar na jahar Adamawa, Alhaji Bilal ya ce sun kira wannan taron zantawa da dattijen jam’iyyar ne domin hakan na daya daga cikin irin dokokin da jam’iyyar ta tsara domin gyaro wadansu wajaje idan akwai. Bilal ya ce sai an sami kalubale da nasarori da kushewa a kowace jam’iyyar sannan ake samin gyara domin cigaban jam’iyyar.

Haka kuma Gwamnan Jahar Adamawa, Muhammadu Jibrilla Bindow ya ce, gwamnatinsa ta yi iya kokarinta wajen gina hanyoyi da dama da gyara makarantu da taimakawa wajen kiwon lafiya da kuma sana’u da ake koyawa matasa domin su iya rike kansu a shekarun biyun farkon da ya yi a jahar.

Mataimakin gwamnan jahar Adamawa, Injiniya Martins Babale wadda ya wakilci gwamna a taron ya yi alkawarin samo wata hanya domin taimakawa mambobin jam’iyyar APC na jahar, sannan ya sanya shugabancin jam’iyyar da ta rubuto wani tsari wadda tafi dacewa ta yadda za su taimakawa mambobinsu domin jin duminsu a mulki.

A cikin wadanda suka halarci taron akwai, Sanata Binta Masi Garba da tsohon minista, Alhaji Abdulrahman Adamu da tsohon Babban Darakta, Alhaji dahiru Bobbo da sauransu.