✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

dauki-doran ’yan takara ne babbar matsalar PDP a Yobe – Haruna Waziri

Alhaji Haruna Bawa Waziri jigo ne a Jam’iyyar PDP kuma daya daga cikin ’yan takarar Sanata daga mazabar Yobe ta Kudu a karkashin jam’iyyar, a…

Alhaji Haruna Bawa Waziri jigo ne a Jam’iyyar PDP kuma daya daga cikin ’yan takarar Sanata daga mazabar Yobe ta Kudu a karkashin jam’iyyar, a tattaunawarsa da wakilinmu ya ce yadda ake neman dauki-doran ’yan takarar jam’iyyar ba tare da zaben fidda gwani ba, na iya kassara jam’iyyar a kokarin da take yin a kwace gwamnati daga hannun Jam’iyyar APC a Jihar Yobe:

Aminiya: Za mu so ka gabatar mana da kanka?
Haruna Waziri: Sunana Haruna Bawa Waziri, ni neman tsayawa takarar Sanata ne a karashin Jam’iyyar PDP daga mazabar Yobe ta Kudu (Zone B) a Jihar Yobe.
Aminiya: Ka ce kai me neman Sanata ne, wannan ba yana nufi ba a gudanar da zaben fidda-gwani ba ne a yankiku?
Haruna Waziri: A saninmu ba a yi zaben fidda gwani na sanatoci ba har yanzu a Jihar Yobe, musamman a yankin da nake, ban sani ba ko an yi a sauran amma a yankina ba a yi ba. Muna nan kuma muna jira a Yobe ta Kudu
Aminiya: Me ya hana a gudanar da zaben fidda gwanin?
Haruna Waziri: To, ba mu san abin da ya hana ba, abin da na sani shi ne a lokacin da muka sayi fom na nuna sha’awa da na tsayawa takara na PDP sun ba mu jagorar zabe na jam’iyya, suka ce mu jira za a kira mu wurin tantancewa, in mun haye tantancewa za a kira zaben fidda gwani. To gaskiya mun zauna ni da mutanena muna ta jira a kira mu tantacewa zuwa zaben fidda gwani, ba mu ji komai ba. Har wasu jihohi suka kira aka tantance aka yi zaben fidda gwani, amma mu ana cewa har yanzu tukunna, tukunna. Tukunnan nan shi ne har yanzu muna jira.
Aminiya: Ke nan kana nufin cewa Jam’iyyar PDP ba ta mika wa Hukumar Zabe dan takarar Sanata daga mazabarku ba?
Haruna Waziri: To, wannan kuma wata tambaya ce. Gaskiya a sanina babu dan takara tukunna dai, saboda zaben fidda gwani ne yake fito da dan takara. Lokacin da muka sayi fom sun nuna mana cewa a cikin tsarin mulkin PDP ga hanyar fito da dan takara ga kuma hanyar da ake bi, ko daya ba a yi ba. To in wani ya fito ya ce shi ne dan takara, to mu ba mu sani ba, domin ba mu ji an yi zaben fidda-gwani ba, kuma ba mu ji Hukumar INEC ta fito da dan takarar Sanata daga Yobe ta Kudu ba. Shi ya sa muke cewa har yanzu muna nan muna jira, kuma mun rubuta kuka ga uwar jam’iyya. Domin jam’iyya ta ce in kana da korafi kan wani abu da yake faruwa ka rubuta mata, to mun rubuta wa Shugaba da Sakatare da Mashawarci kan Shari’a na Jam’iyyar PDP ta kasa da sauran wadanda ya kamata a rubuta musu. Ni da wasu ’yan takara mu rubuta musu kuka, cewa mun sayi fom har yanzu fa ba a yi zaben fidda gwani ba, me ke faruwa? Amma har yanzu ba mu ji komai daga gare su ba.
Aminiya: A tunaninka me kake ganin ya kawo haka din?
Haruna Waziri: To, abubuwa da yawa suke faruwa a Jihar Yobe, domin mun ji cewa ban da namu na sanatoci da sauran ’yan majalisa, har yanzu akwai matsalar da take tafiya a bangaren masu neman Gwamna a jihar. Yana daya daga cikin abubuwan da muke tunani watakila shi ya sa har yanzu ba a yi zaben fidda gwani a jihar ba, saboda masu neman Gwamna su ma suna kukan cewa zaben fidda gwanin da aka je aka yi bai yi daidai ba. Kwanan baya jaridu sun buga cewa Mataimakin Shugaban kasa yana kokarin ya sulhunta tsakaninsu, daga baya muka ji cewa biyu daga cikinsu ba su amince da sulhun da aka yi ba. To, wadannan abubuwa da suke faruwa muna ganin shi ya sha gaban namu din. To amma nasu na Gwamna ne mu kuma namu daban yake saboda haka muka ce ba za mu yi shiru ba, gwanda mu tuntuba mu ji me yake faruwa? Shi ya sa muka rubuta wa hedkwatar jam’iyya cewa ga abin da yake faruwa, mun sayi fom ba mu ji an yi komai ba. Kuma mun dauki matakin zuwa kotu cewa ba a yi mana zaben fidda gwani ba, yanzu muna jira kotu ta yanke hukunci kan abin da ya kamata a yi.
Aminiya: Akwai alamun jam’iyyarku a Yobe na fama da rikici a tsakanin, bangaren Adamu Maina Waziri da Yarima Lawan Ngama, ba ka ganin rikicin ne ke jawo muku matsala?
Haruna Waziri: Ina son in shaida maka ba su biyu kadai ne ’yan takara ba, su hudu ne, akwai Alhaji Ibrahim Talba, akwai Hassan Kafayos su ma suna takarar. daya daga cikin da ya faru a makon jiya da Mataimakin Shugaban kasa ya je yana kokarin sulhu, sulhun nan ya tsaya ne tsakanin Alhaji Maina Waziri da Alhaji Ngama. To su kuma Alhaji Ibrahim Talba da Hassan Kafayos sun fito a jarida suka ce, ba wanda ya tuntube su, an maida su kamar ba su cikin ’yan takara alhali matsalar da ta faru ba a tsakanin Waziri da Ngama ba ne kawai har da su a ciki, don haka ya kamata su ma a kira su, in ma sulhun za a yi ya zamo suna ciki.
Aminiya: Misali da za a ce an yi zaben fidda-gwani a shirye kuke ku dafa wa wanda ya samu nasara?
Haruna Waziri: Insha Allahu za mu dafa masa, domin Allah Yake bada mulki da matsayi, amma mu abin da muke magana a yi adalci. Amma in aka ce kawai an je a sanya wani daga sama ne wannan ba adalci, kuma zai kawo mana matsala.
Aminiya: Idan aka lura a Jihar Yobe kamar wadanda ya kamata su zamo dattawa su ne a tsakaninsu suke rigima, ba ka ganin shi ne yake kuke cikin matsala?
Haruna Waziri: Gaskiya dattawan PDP a Yobe wasu daga cikinsu sun yi kokarin su magance wannan lamari kafin ya tsama matsala, amma ka san in kana son ka yi maganin abu, sai da yardar kowa.
Aminiya: A matsayinka na dan takarar da kake ganin ba a yi muku adalci ba, wani mataki kake gani za kawo muku maslaha?
Haruna Waziri: To, daga farko dai lokacin tsayar da dan takara ya wuce, kuma ba mu sani ba ko Jam’iyyar PDP tana da wata mafita da za ta bi a kan wannan matsala. Domin ina ganin ba Yobe kadai ba ne, amma matsalar ta Yobe ta bambanta, domin ko zaben fidda gwani ba a yi ba. Wasu an yi alamar zaben fidda gwani ana sulhuntawa da wadanda suka fadi da wadanda suka ci, amma mu namu ko irin wannan ba a yi ba. To ni a matsayina na mai neman Sanata na san komai yana da ka’ida komai na karkashin shari’a a Najeriya, shi ya sa muka ce to tunda abin ya zama haka, bari mu je mu nemi hakkinmu a kotu, watakila kotu za ta gaya wa jam’iyya ga abin da ya dace. Domin mun rubuta wa jam’iyya don ta shiga ta sulhunta ba a ce mana komai ba. Mu kukan da muke yi har muka je kotu muna bukatar a je a yi abin da dokar jam’iyya ta ce a yi ne. In muka fadi kuma muka ga akwai hanyar kuka za mu yi, kawai mun sayi fom muna jira a tantance mu shiru, daga baya muka ji an fara tantacewa a wasu jihohi mu shiru, aka yi zaben fidda gwani mu nan Yobe shiru ba mu ji komai ba, ba wanda muka ji komai daga gare shi, ka ga akwai ayar tambaya a kan wannan. Daga baya sai muka rika jin jita-jita cewa an kai sunan wasu a matsayin ’yan takara, ba mu sani ba, muna fata ba haka ba ne. Domin idan aka yi haka, an yi babban zalunci, kuma in aka yi zalunci inda mutum zai nemi hakkinsa shi ne kotu.
Aminiya: Ga alama a iya cewa kusan kun rasa wannan kujera ke nan, tunda ba a yi zaben fidda gwani ba. Ke nan in kun rasa wannan dama mene ne matakin bi nag aba?
Haruna Waziri: Ka san dadin abin kotu ce mai yanke hukunci na karshe tunda mun tunkare ta, idan kotu ta ce wa jam’iyya ta je ta zaben fidda gwani ita ma Hukumar INEC tana bin dokar kasa ce, dokar kasa kuma kotu ce mai fassara ta. Don haka muna ganin cewa har yanzu akwai alamar za a iya zaben fidda gwani yadda ya kamata, idan kotu ta ce a je a yi, idan kuma ta bada wani hukunci na daban za mu amince da abin da ta ce.
Aminiya: Wace kira kake da ita ga jam’iyyarku ta PDP kan wannan matsala?
Haruna Waziri: Ga mutanenmu na yankin Yobe ta Kudu, mu PDP muke yi. Amma saboda wadannan rigingimun da rashin adalcin da ke gudana, sun sa gaskiya mutane suna tunanin su kuma wani waje. Mu abin da muke kokari mu nuna musu shi ne cewa ba haka ba ne. Akwai yadda za a yi a gyara wadannan abubuwa. Don haka ina kira ga jam’iyyar nan tamu ta PDP, su yi tunani su duba abin da ya faru. Inda za a gyara a gyara, inda ba za a iya gyarawa ba a kira mutane a yi musu bayani kowa ya fahimci abin da yake tafiya. Amma irin wannan abin da ake yi na dauki-dora a kan jama’a, shi ne gaskiya yake kawo mana matsala. Ba zan ce gaba daya haka lamarin yake a kasar nan ba, amma banagaren da nake kuma na sani nake fafutika, ina ganin matsalar ke nan, don haka a dawo a yi adalci. Jam’iyyar nan ta kowa ce, dimokuradiyya ake yi ba abin mutum daya ba ne. Ina ganin ya kamata duk mai ruwa da tsaki a zauna a samu yarda. Ga shi muna dab da zabe bai wuce mako biyar a yi zabe ba, amma ga irin tafiyar da muke yi, haka ba zai yi mana kyau ba, gaskiya fisabilillahi.
Aminiya: Ko kana da sako ga su jama’ar mazabarka?
Haruna Waziri: Sakona ga jama’ata shi ne, na san rashin adalcin da aka yi ya dame su kwarai da gaske, amma duk da haka ina kira su yi hakuri tukunna. Komai ya yi zafi zai yi sanyi, mu jira mu ga abin da kotu za ta ce, idan mu ne muka yi nasara, Alhamdulillah, sai mu dawo mu san shirin da za mu yi, idan kuma ba mu ba ne, nan ma Alhamdulillah za mu amince da abin da ta yi.