✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daure mashaya wiwi ba ya da alfanu – Obasanjo

Tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya yi kiran a daina daure kananan mashaya tabar wiwi, inda ya ce hakan yana mayar da su manyan…

Tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya yi kiran a daina daure kananan mashaya tabar wiwi, inda ya ce hakan yana mayar da su manyan masu aikata laifuffuka.

Cif Olusegun Obasanjo ya shaida wa BBC cewa a lokacin da aka daure shi a gidan yari ya hadu da mutane da dama wadanda laifinsu bai wuce “Kama su da kullin wiwi ba, amma aka daure su.”

A cewarsa, “Idan matashi ya soma shan wiwi kuma aka kama shi aka daure a gidan yari zai fito a matsayin babban mai aikata laifi. Maimakon haka, ya kamata a ba su kulawa ta musamman; a ji ta bakinsu, a rarrashe su domin su daina yin abin da suke yi.”

Tsohon Shugaban kasar yana magana ne a daidai lokacin da wata kungiyar yaki da tu’ammali da miyagun kwayoyi ta duniya, mai suna The Global Commission on Drug Policy – wacce fitattun shugabannin duniya ke cikinta, ta yi kira a sake yin nazari a kan yadda ake magance matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi.

kungiyar, wacce ta fitar da sabon rahoto a kan yadda ake tunkarar yaki da miyagun kwayoyi, ta ce tsangwamar da ake yi wa masu shaye-shayen kwayoyin tana yin kafar ungulu a yakin da ake yi da miyagun kwayoyin.

Cif Olusegun Obasanjo shi ne shugaban kungiyar reshen Afirka ta Yamma.