✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Denmark za ta janye dakarunta daga Mali

Daman babu amincewar zuwan sojojin daga hukumomin Mali.

Denmark ta ce za ta soma janye dakarunta daga Mali bayan sojojin rikon kwarya a kasar a makon nan sun matsa kan janye dakarun nan take.

Faransa da kawayen kasar na Turai a baya sun bukaci Mali da ta bar dakarun Denmark din su tsaya, sai dai matsin lambar da Mali ke yi kan sojojin su tafi ana kallonsa kamar rashin kunya ga Faransa.

A daren Laraba, gwamnatin sojin Mali ta bayyana cewa “babu amincewar zuwan sojojin daga hukumomin Mali.”

Denmark ta tura dakarunta har 105 zuwa Mali a ranar 18 ga watan Janairu domin haduwa da dakaru na musamman na Turai wadanda ake kira Takuba wadanda aka kafa domin taimakawa wajen dakile masu ikirarin jihadi.

Rashin jituwa ya kara tsananta tsakanin Sojojin Mali da Faransa

Faransa na kara azama wajen tattaunawa da kawayenta na Turai a game da dambarwar da ke tsakaninta da kasar Mali da ke fama da tashin hankali, wadda ke barazanar rikidewa zuwa rikici tsakaninta da gwamnatin sojin Bamako.

A shekarar 2020 ne Faransa  ta kafa rundunar hadin gwiwa ta Takuba, da zummar jan hankalin kawayenta na Turai wajen daukar wani bangare na nauyin yaki da ta’addanci a Mali.

An samar da gamayyar, wadda ta tattaro dakaru na musamman  daga kasashen Turai a karkashin jagorancin Faransa don  bada shawarwari ga sojojin Mali, tare da taimaka musu a fagen daga.

Al’amuran da suka auku a baya bayan sun sa dakarun Takuba sun karu zuwa dari 9, amma makomar aikin na samun cikas sakamakon gutsiri   tsoma tsakanin Faransa da Mali.

Rikicin da ya kunno kai tun bayan juyin mulkin Mali na watan Agusta ya zafafa, musamman tun da sojojin Mali din suka sanar da dauko sojojin haya daga Russia, matakin da Faransa ta nuna ba ta so.

Matsalar  baya bayan nan ya kunno kai ne lokacin da Mali ta bukaci dakarun Denmark da suka sauka kasar don aikin rundunar Takuba su koma, bisa dalilin cewa an gayyato su ba da saninta ba.

Ministar Tsaron Faransa  Florence Parly ta caccaki wannan mataki, wanda ke zuwa mako guda bayan Mali ta nemi a sake nazarta yarjejeniyar tsaro da ke tsakanin kasashen 2.