Direbobin bas din safa-safa ne da ke aiki a tashar bas din CMS da yawansu ya kai 500, suka amfana da shirin kula da lafiya da gwamnatin Jihar Legas ta bayar kyauta.
Direbobin sun amfana da gwaje-gwajen da suka hada da na hawan jini da ciwon suga da duba idanu da kuma duba zazzabin cizon sauro, tare da ba su shawarwari da wasu magunguna.
Kwamishinan kiwon lafiya na jihar, Dokta Jide Idris ya ce ma’aikatar lafiya ta jihar ta samar da wannan shirin ne, domin ganin an inganta lafiyar direbobi, don taimaka wa sana’arsu ta jigilar mutane daga wannan sashen jihar zuwa wancan, ta yadda za a taimaka wa fasinjojin da rage hadurra.
Dokta Idris, ya ce baya ga duba su haka, kuma an yi musu lacca game da muhimmacin kula da wadannan cuttuttukan lokaci-lokaci, domin ta haka ne za su kare kansu.
Kwamishinan ya shawarci direbobin da su daina shan giya, domin shan giya na kara habaka cututtukan da aka yi musu gwaji, ta yadda za su kiyaye wasu dokoki ko kuma sharuddan kula da lafiya. “Saboda gudunmuwar da direbobi ke bai wa al’umma ya sa ma’aikatarsa tare da hadin gwiwar ma’aikatar sufuri ta jihar da kamfanin giya mai yin ginis suka samar da shirin wayar da kan direbobin,” inji shi.
Wannan shirin, shi ne irinsa na farko, a cewar kwamishinan, don haka suke fatan karade daukacin fadin jihar.
Direbobi 500 sun ci gajiyar kula da lafiya kyauta a Jihar Legas
Direbobin bas din safa-safa ne da ke aiki a tashar bas din CMS da yawansu ya kai 500, suka amfana da shirin kula da lafiya…