✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Doka a Kaduna: Yadda matafiya suka makale a Barde

Wasu matafiya daga Abuja zuwa Jos babban birnin jihar Filato da Bauchi da wasu jihohin Arewa Maso Yamma, sun makale ranar Juma’a a wuraren biciken…

Wasu matafiya daga Abuja zuwa Jos babban birnin jihar Filato da Bauchi da wasu jihohin Arewa Maso Yamma, sun makale ranar Juma’a a wuraren biciken ababen hawa da ke hanyar Keffi zuwa Barde.

Hakan ya faru ne bayan da Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24 daga ranar Alhamis 26 ga watan Maris 2020.

Binciken Daily Trust ya tabbatar da cewa matafiya da dama ne sojoji suka hana wucewa daga shingayen binciken.

Sojojin sun sanar da jama’ar cewa an sanya dokar hana fita a Jihar Kaduna don haka suka umarce su da su canza hanya.

Daya daga cikin matafiyan mai suna Adamu Toro, wanda yake hanyarsa ta zuwa Bauchi da misalin karfe 9:30 na safe ya sanar wa wakiliyarmu ta wayar salula cewa, akwai matafiya daga Abuja da suke hanyar zuwa jihohin da suka hada da Filato, da Bauchi, da Gombe, da Yobe, da kuma jihar Borno, wadanda a lokacin suka yi cirko-cirko a shingen binciken da ke hanyar garin Keffi zuwa Barde.

Adamu ya kara da cewa shi da abokan tafiyarsa rufe hanyar ya sa suka canza wata hanya, inda suka bi ta Lafiya babban birnin jihar Nasarawa sannan suka shiga ta Kudancin Filato cikin garin Shendam.

“Mun yanke shawarar sauya hanyar ne saboda sojojin sun hana mu wucewa, kuma mun dade a shingen binciken”. inji shi.