✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Doya-Hamsin ga ’yan Majalisar Nasarawa: Aiki muka tura ku majalisa ba fada ba

Wani jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Nasarawa Alhaji Usman Adamu Doya-Hamsin ya bukacin ’yan Majalisar Dokokin Jihar su maida hankalinsu wajen kirkiro dokoki tare…

Wani jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Nasarawa Alhaji Usman Adamu Doya-Hamsin ya bukacin ’yan Majalisar Dokokin Jihar su maida hankalinsu wajen kirkiro dokoki tare da tabbatar da ana aiwatar da dokokin da za su kawo ci gaba da canji mai ma’ana ga rayuwar al’ummar jihar maimakon su rika fadace-fadace a tsakaninsu.
Alhaji Usman Doya-Hamsin ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a Lafiya, inda ya ce rigirgimun da suka auku a tsakanin mambobin majalisar a kwanakin baya har suka kai ba hamata iska ya zubar da mutuncinsu da na Jam’iyyar APC a jihar kasancewar jam’iyyar ce ke da rinjaye majalisar.
Ya ce duniya ta yi tir da wannan mummunan lamari, “Ina so in tunatar da ’yan majalisarmu idan sun manta, cewa mun turo su majalisa ne don su yi mana aiki ba don su yi fada da junansu ba. Mun san dole ne su samu rashin jituwa tsakaninsu, amma ya kamata duk lokaci da haka ya auku su sulhuta kansu ba tare da an samu tashin hankali ba. A gaskiya abin da suka yi ya zubar da mutuncinsu da jam’iyyarmu ta APC da jihar nan a idon duniya. Sabada haka ina kira gare su don Allah su maida wukakensu cikin kube su rika hawa taburin sasantawa a tsakaninsu da bangaren zartarwa don magance duk wata matsala da ta taso domin amfanin al’ummar jihar da suka zabe su,” inji shi.
Alhaji Doya-Hamsin ya yi kira ga bangaren zartarwa ya tabbatar yana yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da dorewar kyakkyawar dangantaka tsakaninsa da majalisar, ya ce bangarorin biyu suna aiki ne don ci gaban jihar.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne aka samu rashin jituwa tsakanin bangaren zartarwa da na majalisar game da nadin shugabannin rikon kwarya da za su maye gurbin tsofaffin shugabannin kananan hukumomin jihar da wa’adinsu ya kare, inda ya kai ga ba hammata iska a tsakanin ’yan majalisar.