✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dumamar yanayi (1)

A da an sam sauyin yanayi, wanda ya sa mutane suke tashi daga wasu wurare zuwa wasu wuraren, har suka tsinci kansu a inda suke…

A da an sam sauyin yanayi, wanda ya sa mutane suke tashi daga wasu wurare zuwa wasu wuraren, har suka tsinci kansu a inda suke a yau! Yanayi kan sauya a bisa wata masifa kamar zaizayar kasa, kwararowar Hamada, kankancewar koguna, ambaliyar ruwa, fari ko yaki, balle sauyin yanayi, inda damina kan ja baya ko teku ya kara cika, ya batse iyakoki, ya ci kasa. Ci gaban yau ya kai har ana gini a kan ruwa, duk da ba a taba samun zamanin da aka rika tuna kasa, yashe kasan kasa, da yanke itatuwa ba, kamar wannan zamanin!.

Hasashe yanayi na daya daga cikin abubuwan da suka fi wahala a ilimin zamani, musamman ilimin gane sauyin yanayi. Yayin da sakamakon sauyin yanayin ya haifar da mutuwa da raguwar halittu, musamman dabbobo kamar kuraye, kada da macizai, daga ja da baya, sai su bace! Yaushe rabon da a ga damisa a Yankari cikin Jihar Bauchi, Giwaye ma na fuskantar barazana! An kiyasata cewa kowace shekara sai wasu dabobi sun bace, a bisa yadda bil-adama yake gurbata yanayi da kazanta. Ana fuskantar wahala wajen binne kwata, wadda wani lokacin a ruwa ake zuba dagwalon watau a tsakar teku, a saki gubar wadda za ta kashe kifaye da mayar da ruwan wani kunu mai kauri, wanda wasu jiragen ruwan kan makalle da zarar sun shiga wannan kwata.

daya daga cikin manyan abubuwan da suke sa yanayi ya sauya a yau, shi ne cewa  rana na dukan duniyar, wanda yake ba shuke-shuke da tsirrai damar girma da sarrafa abincinsu ta hanyar ruwa, haske da iskar da muke fitarwa (Carbon diodide). Yayin da sai su fito da iskar da muke shaka (Odygen), shi ya sa in ka shiga karkashin inuwar bishiya za ka ji iska na kadawa mai dadi, yayin da yadda ake yanke itaciyoyi da rashin shuka wasu bishiyoyin yake kawo wannan sauyin cikas, a haka ne masana fasaha suka ce duniyar za ta zama kamar wani koren gida, wanda iska ba za ta iya sauyawa ko kewayewa ba, musamman in mun duba cewa akwai hayakin kamfanoni da motoci da babura da gidaje, wannan zai kara dagule matsalar samun iska mai kyau, sannan babbar matsalar sauyin yanayi ita ce a inda ake yawan zafi ko zafin ya yi tsananin ko a fara sanyi, haka za a yawaita samun ambaliyar ruwa domin narkewar kankara a sama da kasan duniya. Sauyi da gurbata yanayin ya jawo karewar kifaye da wasu hallitun ruwa wanda suke rayuwa a gabar teku a Turai da wasu sasan duniya.

A wasu sassan duniyar a kan samu sauyi biyu a shekara watau zafi da ruwan sama, yayin da kafin a yi ruwan sai zafi ya zo, wanda zai tafasa ruwan da yake kasa, wannan ruwan yake tafiya sama a wata urun fasaha, watau abin da ake kira turirin iska (Ebaporation), sai ya shiga wani yanayin sauyi a giza-gizai, bayan wannan harka, sai ruwa ya sauko, kuma bayan damina sai holoko ya share wa sanyin hunturu hanya. Sannan a wasu sassan a kan sauya yanayi sau hudu kamar zafi lokacin faduwar ganye daga kan itacen ciyawa ta zama dorawa, a lokacin ake zuwa bakin teku a sha iska, ko a tafi kasashen da suke da zafi don a sha rana, tun daga Yuni har zuwa Satumba, sannan sai ruwan sama, bayan haka sai sanyi, sannan sai sabon iska ka kara kadawa kafin ya tofo da itace, watau tsakanin sanyi da zafi, da zafi ake samun dogon hutu a Turai, watau wajen Maris har zuwa Yuni, a wannan lokacin an fi yin guguwa a yankin Turai da Amurka wato tsakanin Mayu zuwa Satumba, a wasu kasashen ba a ruwan damina, sai dai ruwan sama, da sanyi domin daskarewar kankara a sama.

Daga nan sai lokacin da ke tsakanin zafi da sanyi ya kewayo, watau a lokacin tsawon rana na gajarcewa, sai dare ya yi tsawo, sannan iskan sanyi-sanyi na kadowa, kafin sanyin a wasu wurare kankara ta sauko, a wannan tsakanin ne ake girbi, kafin a yi shirin zaman gida da sanyi, kuma ko dabobi na da irin wannan dabi’ar, yayin da za su tara gyada su boye domin sanyi, musamman kurege da cinaku suma suna da irin wannan baiwa ta nema da ajewa don wata rana.

Mutane kan taka rawa wajen sauya yanayi, ta hanyoyin hallaka dabi’a don biyan bukata, kamar yanke itatuwa da ciyayi, cike kududdufi, da kona daji don kamun bera da burgu da damo da macizai, a haka ya zama ko a yau angulu (wadda ake kira kazar sama) ta bace a kasar Hausa, sannan ko da damina babu dodon kodi, shi kanshi jan kwaron nan damina ya fara bankwana, wata rana za a neme shi a rasa! Ina beran Masar, ko sun koma Masar?

Akwai damuwa da tashin hankali kan yadda ake gani tafkuna da koguna na tsotsewa da kankancewa, ba tare da gabatar da dokar ta-baci ba kan ruwa. Ba a yashe rijiyoyi, sannan gina rigijojin burtsatse a kowane gida, yayin da rijiya daya tai she unguwa ko gari guda sai ka iske kowa na huda kasa, ta janye rowan, ya ki ba makwafcinsa, sai dai shi ma ya huda! Cike kududdufai da toshe magudanan ruwa, hakan kan kara kawo barazanar ambaliyar ruwa da tunzurin teku.

Masana kiwon lafiya sun tashi tsaye wajen ganin an samu yadda za a iya samun magani cikin gaggawa don tunkarar irin wannan matsalar da ake tsamanin zuwan ta wata rana, domin ko cutar zazzabin kaji ko murar aladu ta isa a yi la’akari da irin abin da yake tafe a duniyar da aka cunkushe abubuwa, sannan mutum ya zama shi ne makashin kansa, domin ya kirkirowa kansa abin da zai zama illa ga rayuwarsa, abin da zai rage masa karfi a dabi’ance, ko a abinci da dabi’ar tafiyar da rayuwa, wadda ta haifar da kasala. Wannan duk su suka zama abubuwan da suke dumamar yanayi a dogon zango, kamar tsarin kona itatuwa da man fetur da fitowar hayaki daga manyan masana’antu, abin da gasa ta sa kamfanonin da suke gasa a kasashe masu ci gaba, tsakanin nahiyoyi don samun matsayi a doron duniya.

 

Buhari Daure [email protected] Modoji, Katsina