✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dutse mai aman wuta na ci gaba da barna a New Zealand

’Yan sanda a New Zealand sun ce har yanzu babu wata alamar cewa mummunan yanayin da ake ciki a Tsibirin White Island ya canja don…

’Yan sanda a New Zealand sun ce har yanzu babu wata alamar cewa mummunan yanayin da ake ciki a Tsibirin White Island ya canja don haka ba za a iya gudanar da aikin ceto sauran wadanda suka makale a tsibirin ba, bayan fashewar wani dutse mai aman wuta a ranar Litinin. ’Yan sandan sun ce kimanin masu yawon bude ido 50 ne ke ziyartar tsibirin na White Island lokacin da wani sashi na tsaunin ya tarwatse bayan soma aman wutar.

Sufeton ’Yan sanda Bruce Bird ya fada wa ’yan jarida cewa suna ci gaba da duba yiwuwar shiga tsibirin da zarar sun samu dama. To amma Ministan ’Yan sandan New Zealand ya sanar da cewa har yanzu akwai gurbataccen hayaki da ke ci gaba da bazuwa a tsibirin.

Jami’an sun ce akalla mutum 24 ake fargabar sun hallaka, yayin da wadansu 23 suka tsira da raunukan kuna. Tuni dai jami’an agaji suka ce sun fid da ran ceto karin wadansu mutane da aman wutar dutsen ta rutsa da su, bayan shafe tsawon lokaci ana lalube da jirage masu saukar ungulu.

Tsibirin White Island da aka fi sani da Whakaari, shi ne yankin da ke kan gaba wajen fuskantar aman wutar dutse a kasar New Zealand, inda kididdiga ta nuna cewa, akalla masu yawon bude ido dubu 10 ke ziyartar tsibirin duk shekara.

Sanarwar da Firayi Ministan Kasar Jacinda Ardern ta fitar ta shafin sada zumunta ta bayyana cewa a lokacin da dutsen ya yi wata bindiga akwai kimanin mutum 50 a tsaunin. Ta ce mutum 23 sun jikkta sakamakon lamarin, yayin da wadansu suka rasu.

“Ga wadanda suka rasu ko ’yan uwansu suka bata da abokansu, mun yi tarayya cikin bakin ciki wanda ba zai misaltu ba,” inji Jacinda Ardern.

Ta ci gaba da cewa mutum 47 da suke tsibirin a lokacin da dutsen ya barke da aman wuta a ciki har da ’yan New Zealand da dama, da kuma baki masu yawon bude ido daga kasashen Austireliya da Birtaniya da Amurka da China da kuma Malaysiya.

Ardern ta ce ana ci gaba da ayyukan kubutar da wadansu mutum 27 da ke tsibirin. Tun farko ta ce tana fatar ganin ’yan sanda sun samu shiga yankin. Ta kuma ce babban abin da ke gaban masu aikin ceto a yanzu shi ne su ga cewa an ceto rayukan wadanda suka jikkata da ke asibitoci daban-daban a fadin kasar.

Wasu alkaluma sun nuna cewa ’yan sandan kasar sun ba da tabbacin cewa, mutum 31  suna asibiti kuma sun tabbatar da mutuwar mutum biyar.

Rahotanin Kamfanin Dillancin Labarai na AFP da kyamarori suka nuna abin da ya faru kai-tsaye daga aman wutar da dutsen ya yi ya nuna wani rukunin masu yawon bude idon suna tafiya a bakin dutsen kafin ya fara aman wuta. Kawo yanzu an tabbatar da mutuwar mutum shida kuma gwammai sun jikkata, yayin da ake kan neman wadansu da dama.