✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Enugu Rangers ta kori kocinta bayan shan kashi

Ranar Lahadin da ta gabata ne masu ruwa da tsaki a kungiyar kwallon kafa ta Enugu Rangers suka sallami Kocin kungiyar mai suna Benedict Ugwu…

Ranar Lahadin da ta gabata ne masu ruwa da tsaki a kungiyar kwallon kafa ta Enugu Rangers suka sallami Kocin kungiyar mai suna Benedict Ugwu tare da duk daukacin masu dafa masa baya, bayan da kungiyar ta yi rashin nasara karo na uku a jere a wasannin da aka fara gudanarwa a Gasar Firimiya ta kasa ta 2019/2020 da Hukumar wasa ta kasa (NPFL) take shiryawa.

Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Enugu, Bitus Okechi shi ne ya bayyana sallamar kocin bayan da Enugu Rangers ta sha kashi a gida da ci 2-0 a hannun kungiyar kwallon kafa ta Akwa Starlets (Dakkada) FC ta garin Akwa Ibom.

An bai wa Ugwu rikon kwaryar horar da ’yan wasan kungiyar ne tun a watan Yuli, bayan karewar wa’adin kwantaragin Koci Gbenga Ogunbote, wanda ya tafiyar da ragamar kungiyar daga 2017 zuwa 2019.

A halin yanzu tsohon dan wasan Najeriya, Sylbanus Okpala, shi ne ya karbi ragamar kungiyar daga hannun tsohon Koci Benedict Ugwu wanda ake wa lakabi da ‘Surugede’.

Okpala, wanda ya horas da kungiyar Rangers a baya, ana sa ran zai jagoranci kungiyar da ake wa lakabi da Flying Antelopes zuwa ga nasara a gasar cin kofin kungiyoyin Afirka na bana.

Rangers ta kasa cin wasanni uku da ta buga a jere a gasar da ake fafatawa ta kasa.

Kungiyar MFM ta ci Rangers 1-0 a wasansu da suka buga na farko a Enugu sannan kuma ta sha kashi a hannun Ribers United a wasanta na biyu a garin Fatakwal kafin kuma daga baya Akwa Starlets ta lallasa ta da ci 2-0.

Femi Abayi na Akwa Starlets shi ne ya fara jefa kwallo a ragar Rangers a cikin mintina 16 da fara wasa, kafin daga bisani Isaac George ya sake cin su a minti na 43.

Kyaftin din Akwa starlets, Aniekam Ekpe, ya bayyana cewa dama sun shirya sarai don ganin sun yi wannan nasara.

“Nasarar da kungiyar “MFM ta samu a kan Rangers ita ce ta ba mu kwarin gwiwar kai wa ga wannan nasara.

“Yanzu ba mu jin tsoron haduwa da kowace kungiya da take fafatawa a wannan gasa ta kasa, domin kwallo ta gaji nasara ko faduwa.

“Starlets ta yi canjaras har sau biyu ke nan a wasannin da muka buga a waje kuma za mu ci gaba da samun nasara a wasanninmu na waje.

“Rangers suna da kyau amma dai yau sun ci da gigal, domin tsarin da muka yi ya kai mana,” inji shi.

Ekpe ya ci gaba da cewa kungiyar ta su tana bakin kokarinta na ganin ta tara maki da yawa tun a farko-farkon gasar. “Mun ga kungiyoyin da suka hauro kuma aka fafata da su cikin wannan gasa ta NPFL amma daga karshe sai su fado, don haka wannan irin tashin gishirin andirus din ne muke kokari kauce ma wa,” Ekpe ya fada.