✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Fadar Sarki da Bukka’

Assalamu alaikum Manyan gobe, tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin Fadar Sarki da wata Bukka. Labarin ya yi…

Assalamu alaikum Manyan gobe, tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin Fadar Sarki da wata Bukka. Labarin ya yi nuni ga muhimmancin girmama na gaba da kuma mutunta su. A sha karatu lafiya.

 

An yi wani Sarki mai adalci a wani kauye.  Saboda gaskiya da adalcin ya sa jama’arsa ke matukar jin tsoron aikata ba daidai ba suna kuma girmama sa.

Rannan sai ya ce yana bukatar a gina masa fadarsa kusa da wani kogi. Sai dogarai sukay i na’am da bukatar Sarki suka shiga neman wadanda suka kware wajen gina fadar Sarki.

Bayan lokaci kankane sai aka gama gina fadar sarki a nan ne aka bukaci Waziri da ya je ya ga yanayin ginin kafin Sarki ya kai tasa ziyarar.

Isar waziri ke da wuya sai ya hango wata bukka dab da fadar Sarki. Waziri ya tambayi wadanda suka yi ginin cewa ko sun san mai shi? Domin yana so ya sayi bukkar. Koda suka isa bukkar sai suka tarar da wata tsohuwa. Aka yi da ita ta bar wajen ta ki. A cewarta wannan bukkar ita ce dakinta na farko da ta yi auren farko.

Aka kai kararta wajen Sarki sai ya ce a bar ta a Bukkarta shi kuma zai zauna a tasa fadar babu matsala.

Nan take tsohuwa ta durkusawa Sarki ta ce da shi ‘lallai ya kasance Sarki mai adalci da ma ita ba mutum ba ce. Kuma ta zaci zai yi hukuncin da bai dace ba ne da ta yi maganin masarautarsa”.

Daga nan ta roki gafarar Sarki kafin ta bace.

Da fatan Manyan Gobe za su yi koyi da darasin wannan labari.