✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farashin kaya ya karu zuwa kashi 13.22 a Najeriya

Shi ne karin farashin kaya mafi girma da aka samu cikin wata 28 a Najeriya

Hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya karu zuwa kashi 13.22 a watan Agustan 2020.

Alkaluman da Hukumar Kidddiga ta Kasa (NBS) ta fitar ranar Talata sun nuna wata na 12 ke nan a jere farashin kaya na karuwa tun daga watan Satumban 2019.

Karuwar farashin daga kashi 12.82 a watan Yuli zuwa 13.22 a watan Agusta shi ne mafi yawa a cikin watanni 28 da suka gabata.

Rahoton ya nuna farashin kayan masarufi ya karu zuwa kashi 16% a watan Agusta sabanin kashi 15.48 a watan Yuli.

“Farashin kayan abinci ya karu saboda tashin farashin burodi da hatsi da dankali da doya da nama da kifi da ’ya’yan itatuwa da mai da ganyayyaki”, a cewar NBS.

Rahoton ya ci gaba da cewa, “dukkannin amfanin gona” da ba kayan gwari ba sun karu zuwa kashi 10.52 a watan Agusta daga kashi 10.10 a watan Yuli.

“Hauhawar farashin ta fi yawa a kudin motoci da jiragen haya, asibiti, magunguna, kayan gyaran ababen hawa, da kananan motoci da sauransu”, inji rahoton.