✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ruwan leda ya yi tashin gwauron zabo a Abuja

Ana tsoron barkewar cuta a yayin da aka fara hakura bayan ledan ruwa ya koma N20.

Mazauna birnin Abuja sun fara kokawa bayan farashin ruwan leda ya yi tashin gwauron zabo inda aka koma sayar da leda guda a kan Naira 20 zuwa Naira 30. 

Masu sana’ar sun bayyana cewa yanzu ana sayar wa ’yan sari jaka guda na ruwan leda a kan Naira 200; ’yan tireda kuma suna sayar da leda a kan N20 zuwa N30, jaka kuma N250 zuwa 300.

Wata mai sayar da abinci a unguwar Utako a birnin Abuja, Ime Samson, ta shaida mana cewa, “Yanzu N20 nake sayar da ledan ruwa; a da N100 zuwa N120 muke sayen jaka, amma yanzu ya koma N300 zuwa N350. To nawa ake so mu sayar?”

Ime ta ta kara da cewa yanzu ledan ruwa ya koma N20, a wasu wurare kuma ya kai N30.

  1. Dalilin karin

Tsadar ruwan ta biyo bayan yajin aiki da kungiyar masu sarrafa ruwan leda a yankin Abuja suka gudanar, wanda tun kafin shi ake ta hasashen za su kara farashi.

Tun a lokacin sun yi ta korafin da suke yi game da tashin kayan hadi da rashin kyakkyawan yanayin kasuwanci da suka ce ba zai bari su ci gaba da gudanar da sana’ar tasu yadda aka saba ba.

  1. Barazanar barkewar cuta

Wani mazaunin Abuja, Shuaibu Jibrin, ya koka cewa tashin gwauron zabon na iya haifar da barkewar cututtuka masu alaka da shan ruwa mara tsafta.

A cewarsa, a lokacin da suka tafi yajin aikin wasu mutanen sun koma shan ruwan famfo da na rijiyar burtsatse.

A cewarsa, idan aka ci gaba da haka, ana iya samun barkewar cututtuka masu alaka da shan gurbataccen ruwa.

“Mutum na ne za su iya sayen ruwa a kan N250 zuwa N300? Mutane da yawa na kokawa a kan tsadar. Wane irin kari ne haka? Ina tsoron a samu barkewar cuta domin mutane na iya shan gurbataccen ruwa.

“Ina tabbatar maka nan gaba za a kara kudin ruwan roba, saboda ai da haka aka farawa, a cikin ’yan watannin nan kusa komai an kara farashinsa; Daga burodi zuwa kayan abinci zuwa sabulu da sauransu; Ba ma a maganar tufafi da sauran abubuwan bukata.

“Allah Ya sa dai su ma dillalai ba za su kara nasu farashin ba, domin in ba haka ba, abin sai ya fi na yanzu,” inji shi.

Tun kafin yajin aikin da masu gidajen ruwa suka yi ne suka yi da kokawa game da tsadar kayan hadi da sauran mastaloli da suka ce ba zai bari su ci gaba da gudanar da sana’ar tasu yadda aka saba ba.

  1. ‘Mun kara ne domin amfanin kowa’

Wani mai gidan ruwan leda a yankin Gwagwalada, John David, ya ce: “Mun dawo yajin aiki amma yanzu muna sayar da jakar ruwan leda N200; Ya kamata mutane su fahimci cewa ba za mu iya ci gaba da sayar da ruwa a kan tsohon farashin ba.

“Sanin kowa ne yadda abubuwa suka kara tsada a kasuwanni; farashin leda ya tashi, sannan daga matatar ruwan gwamnati muke sayen ruwa domin mu tabbatar da lafiyarsa.

“Bayan haka akwai abubuwa da dole sai mun yi domin tabbatar da tsaftar ruwan; Saboda haka idan muka ci gaba da sayarwa a kan tsohon farashin karyewa za mu yi — Su kan su mutane ba za su so mu daina sana’ar ba.

A cewarsa, sun fara farashin ne domin tabbatar da ingancin ruwan ledan da aka sha na da cikekken tsafta kuma babu wata barazanar kamuwa da cuta daga gare shi.

Mun tambayi wata mai gidan abinci da muka zanta da ita ko kwastomominta na sayen ruwan a kan sabon farashi.

  1. Hakura da ruwan leda

Sai ta kada baki ta ce, “Eh, suna saya; Wasu sun gwammace su sayi ruwan roba, saboda a lokacin yajin aikin da kyar ake samun ruwan leda.

“A lokacin har jin dadi mutane ke iya idan har za su samu ruwan su saya da tsada. Ina jin shi ya sa suka yi yajin aikin, yanzu ka ga mutane dadi suke ji idan suka samu ruwan, ba maganar farashinsa ake yi ba,” inji ta.

Mun yi kicibus da wata mai sayar da abinci da ta koma ba wa kwastomominta ruwa da ta sanya a wata jarka, maimakon ta ba su ruwan leda, a yankin Kado da ke Abuja, tana ba wa kwastomiminta.

A hakan ma wasu kwastomomin ba su damu ba, saboda samun ruwan ma abin jin dadi ne.

Da muka tambaye ta daga ina take samun ruwan da take ba wa kwastomomin nata sai ta ce: “Ruwan rijiyar burtsate ne, yana da tsafta sosai, ya ma fi ruwan leda da ake yawon sayarwa.”

Ita kuma Misis Monica, da ke sayar da abinci ne a unugwar Wuse, ta ce, “Tun da masu ruwa suka fara yajin aiki na koma sayar da ruwan roba. Ina mamakin me suke so mutane su sha; shin sun dauka kowa ne zai iya sayen ruwan roba?

“Abin ya kai ga wasu mutanen abinci kawai suke ci, ba sa shan ruwa, wanda hakan ba daidai ba ne; Ba wai ba sa son shan ruwan ba ne, amma idan ka ce su sayi ruwan roba sai su ce a’a, saboda ya yi musu tsada sosai.”

Misis Monica ta yi fata gwamnati za ta sa baki a cikin lamarin, saboda akasarin mutane, musamman kwastomominta ruwan da suke sha shi ne na leda.

“Na yi mamakin yajin aikin. Tun da kara farashin suke so su yi, mene ne sai su yi yajin aiki?” inji ta.

Wani wanda ya je sayen abinci a shagonta, Abdul Sule, ya ce: “Ban san inda kasar nan ta dosa ba, kusan komai na neman gagaran talaka, hatta ruwan sha na neman gagarar mutane.

“Ya suke so talaka ya yi a Najeriya? Idan aka ci gaba da tafiya haka, za a sha wahala sosai.

“Idan har da gaske za su rika sayar da jakar ruwan leda a kan N300 ko fiye da haka, mutum nawa ne za su iya saye? Yawancin mutane ba za su iya ba, sai dai su koma shan ruwa daga wasu wuraren”.