✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fargabar cutar coronavirus: An rufe babban shagon kasuwanci a Abuja

Hukumar Bunkasa Gasa daKare Hakkokin Masu Amfani Da Kaya (FCCPC) ta rufe babban shagon kasuwanci mai suna Panda, da yake unguwar Jabi a cikin garin…

Hukumar Bunkasa Gasa daKare Hakkokin Masu Amfani Da Kaya (FCCPC) ta rufe babban shagon kasuwanci mai suna Panda, da yake unguwar Jabi a cikin garin Abuja.

An rufe shagon ne saboda fargar bullar cutar coronavirus wanda take kama da cutar SARS pathogen da ta bulla a wata kasuwar Wuhan a tsakiyar birnin kasar Chana, sannan ta yi sanadiyyar kashe mutum 132 kuma tana ci gaba da yaduwa a wasu kasashen.

Har yanzu ba a samu rahoton bullar cutar Coronavirus a Najeriya ba.

Babban shagon Kasuwanci na Panda, yana daya daga cikin manyan shaguna a Abuja da suke siyar da kayan da suka hada da: kayan ciye-ciye, kayan jarirai, abubuwan sha, kifi na waje da kaji da sauran su.