✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fashi a mota: Fasinja ta kusan jawo a hallaka fasinjoji

Matsalar fashi ta hanyar amfani da motar haya da aka fi sani da “One chance” wadda ta yawaita a Abuja, ta yi kusan jawo a…

Matsalar fashi ta hanyar amfani da motar haya da aka fi sani da “One chance” wadda ta yawaita a Abuja, ta yi kusan jawo a hallaka wadansu fasinjoji da wata mata ta zarga da kasancewa masu fashi a mota ne.

Irin wannan aiki na rashin imani da masu fashi a mota suke aikatawa ya sanya da zarar dubunsu  ta cika, sai  mutane su yi gaggawar hallaka su  ta hanyar daukar doka a hannu su yi ta dukansu sai sun ga ba su motsi. A wasu lokuta ma sukan sanya musu wuta su da motarsu su kone kurmus.

A watan Oktoba da ya gabata ma wadansu mutane sun kone wadansu da ake zargin ’yan fashi a mota ne a karkashin gadar Dutsen-Alhaji da ke Abuja. Hakan ya faru ne bayan da masu acaba suka lura cewa wata mata tana ihu da neman taimako a cikin wata motar haya da take wucewa. Hakan ya sanya suka bi motar tare da shan gabanta daga bisani suka fito da mutanen da suke ciki suka yi masu dukan kawo wuka, sannan suka tura su cikin motar suka sanya musu wuta suka kone su kurmus.

Sai dai a makon jiya wani mai kimanin shekara 60 da ba ya son a ambaci sunansa ya shaida wa Aminiya yadda shi da wadansu fasinjoji biyu da direban wata karamar motar haya suka tsallake rijiya da baya; bayan da wata fasinja da take tare da su a motar ta yi ihu, tana neman dauki tare da nuna su a matsayin ’yan fashi da ke amfani da mota.

Ya ce “Lamarin ya faru ne lokacin da na tsayar da mota daga Dutsen-Alhaji zan je Bwari. Na tarar da fasinjoji uku a cikin motar, mutum biyu a baya sai kuma wata mata a gaba.”

Ya ce bayan ya shiga motar an fara tafiya sai daya daga cikin fasinjojin da ya samu a bayan motar ya fara kawo labarin abin da ya faru da ’yan fashi a makonnin da suka wuce a nan Dutsen-Alhaji. “Haka muka sanya baki muna ta labarin, kowa yana fadar abin da ya ji har da direban. Amma matar da take a zaune gaban motar ba ta ce uffan ba,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa “Haka muka ci gaba da tafiya har sai da muka kai daf da Kwanar Ushafa, kwatsam sai matar nan ta yi wuf ta bude kofa tana ihu, tana kokarin fadowa kasa, yayin da motar take cikin gudu. Ganin haka sai direban ya yi wuf ya jawo ta da hannunsa daya ya rike ta. Ni kuma ganin direba yana kokowa da ita yayin da ta jefa kafarta daya waje tana kokarin ficewa da yake ina zaune  ne a bayanta sai na yi wuf na mika hannu na rike ta.”

Ya ce suna ta kokarin hana ta fita yayin da take ta ihu, wanda hakan ya sanya hankalin direbobi da suke a bayansu ya dawo a kansu. “A haka direbanmu ya samu ya tsayar da motar a bakin titi. Da tsayawar motar sai kawai matar ta fita a guje ta tsallaka zuwa daya gefen hanya tana ihu, tana fadin “wancans, wancans!” Kafin ka ce kwabo wuri ya cika da masu motoci da masu babura. Direbanmu ya fita yana kokarin fada musu cewa mu ba ’yan fashi a mota ba ne, amma ina. Babu mai saurarensa, yayin da muka fito waje sai mutane suka fara kokarin dukanmu,” inji shi.

Ya ce “Da yake Allah Ya sa da sauran shan ruwanmu a gaba, sai ga wata motar ’yan sanda ta karaso. Da zuwansu suka tsaya aka fada masu ana zargin cewa mu ’yan fashin wancans ne. Don haka sai suka tunkare mu yayin da suke kokarin hana mutane su taba mu.”

Ya ce duk kokarin da direban motar da sauran fasinja suka yi don su bayyana wa ’yan sanda cewa su ba barayi ba ne da farko ya ci tura. Domin ba su saurare su ba, watakila ganin yadda matar take ta ihu da kiran wancans.

“A lokacin ma na kasa ko magana, abin da kawai na iya yi shi ne, na sanya hannuna a aljihu na dauko katina na shaidar dan fansho na mika wa dan sandan da yake a gabana. Amma bai ko kalli katin ba kuma bai nuna alamun yarda ba. Har sai da na bude baki na fada masa ni tsohon ma’aikacin gwamnati ne dan fansho kuma fasinja ne a motar nan. Sannan ne wani daga cikin jama’ar da suka taru ya yi Magana, ya ja hankalin ’yan sandan cewa a kamanninmu da shekaruna, ya kamata a tsaya a saurare mu, don yana ganin zai yi wahala a ce mu ’yan fashin wancans ne,” inji shi.

Fasinjan ya ce haka ’yan sandan suka tsare mutane tare da sauraren bahasi daga bakinsa, inda a karshe aka fahimci dukkansu fasinjoji ne da babu wanda ya san wani daga cikinsu. Ya ce “Muna cikin haka sai ga wadansu direbobin tasi da suka san direban da ya dauko mu sun zo sun tsaya, inda suka tabbatar wa ’yan sanda cewa sun san direban ba dan fashin wancans ba ne. Haka ya sa jikin jama’a ya yi sanyi, sai aka juya matar ana yi mata tambayoyi kan abin da ya sa ta ce muna kokarin yi mata fashi ne. Bayan jama’a sun gane kame-kame take yi, ba ta da wata hujja, sai wadansu suka ci gaba da Allah wadai da abin da ta yi. Ganin cewa da a cikin jama’a ne sosai hakan ta faru da babu ma wanda zai tsaya jin ta bakinmu take za a hallaka mu.”

Ya ce direbansu ya yi kokarin lallai sai ’yan sanda sun kama matar nan da wadansu ke ganin watakila ba ta son biyan kudin motar ce ya sa ta yi wannan dabara amma sai jama’ar da suka taru suka yi ta ba shi baki kan ya bar ta da Allah, tunda sun tsallake rijiya da baya.

Fasinjan ya ce, “Wani abu mai kamar haka bai ta taba faruwa da ni ba. Amma ya faru da ’yata wata daya da ya wuce, lokacin da ta hau motar haya daga Nyanya zuwa Asokoro. Kamar yadda ta fada mana, ta samu wadansu fasinjoji a cikin motar kuma jim kadan bayan an fara tafiya sai ta ji kanta yana juyawa. Ta ce ba san abin da ya faru ba sai ta ga kanta a wani daki mai duhun gaske; ita da wata fasinjar da suke motar.”

Ya ce “Mun yi ta nemanta har kwana biyar ba mu samu labarinta ba duk kuwa da yake mun kai cigiya wajen ’yan sanda. Haka ya sanya muka ci gaba da addu’a tare da kara kaimi wajen nemanta. Da farko muna tsammani ko an yi garkuwa da ita ce, to amma da muka ga kwana da kwanaki ba a kira mu ba sai muka fara tunanin wani abu daban ya faru da ita.”

Ya ce yarinyar ta fada masa cewa ta yi kwana biyu tana barci a dakin ba tare da ta farka ba. Bayan nan ne kuma sai ta farka, inda ta ga an daure musu idanu daga nan kuma aka canja mata wuri ita da wacce suke tsare a dakin zuwa wani daki daban. Ta ce a sabon dakin da aka kai su ne suka yi ta yin addu’a, daga baya suka samu suka kwance daurin fuskarsu sannan suka gudu ta fitowa ta tagar dakin. Ta ce bayan sun fito hanya ce suka samu wadansu mutane suka tambaye su inda suke, inda aka shaida musu cewa suna Akwanga a Jihar Nasarawa.

Ya ce har yanzu sun kasa gane abin da ya faru da yarinyar, ganin cewa ba a karbi komai a wajenta ba, inda wadansu ke zargin cewa watakila masu tsafi ne suka kama su.

Ya ba masu hawa motaocin haya shawarar  cewa ya kamata mutane su rika kula sosai da irin motocin da suke hawa, musamman wadanda ba su da lamba ko fentin tasi. Kuma ya ja hankalin fasinjoji su guji shiga motar da wani fasinja zai fito ya ce su fara shiga kafin shi da aka tarar a motar ya sake shiga, don sanya su a tsakiya.

“Jama’a su sani cewa ya zama wajibi kafin ka bar gidanka ka tsaya ka yi addu’ar Allah Ya kare ka kuma ka sanya iyalanka su taya ka da addu’a. Domin kuwa ko da wani abu zai faru da kai sai ka ga ya zo da sauki sosai,” inji shi.