✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

FC Barcelona ce za ta lashe kofin Zakarun Turai – Solskjaer

A ranar Talatar da ta gabata ce kocin Manchester United da ke Ingila Ole Gunnar Solskjaer ya ce ga dukkan alamu, kulob din FC Barcelona da…

A ranar Talatar da ta gabata ce kocin Manchester United da ke Ingila Ole Gunnar Solskjaer ya ce ga dukkan alamu, kulob din FC Barcelona da ke Sifen ne zai lashe gasar Zakarun Turai a bana.

Kocin ya bayyana haka ne jim kadan bayan Barcelona ta lallasa United da ci 3-0 a wasa karo na biyu da suka yi a filin wasa na Camp Nou da ke Sifen.  A jimilla, Barcelona ta doke United ne da ci 4-0.

Solskjaer ya kara da cewa ganin yadda Barcelona take takama da zaratan ’yan kwallon gaba da tsakiyar fili, ya nuna a bana kulob din ne zai zama zakara a gasar.

“Ba zan iya shiga caca a kan FC Barcelona ba, don na san kulob din ne zai lashe gasar ta bana,” inji Solskjaer lokacin da jaridar The Mirror ta Ingila take yi masa tambayoyi.

Magoya bayan Manchester United sun harzuka jim kadan bayan an tashi wasan, inda suka rika caccakar kocinsu Ole Gunnar Solskjaer game da salon wasan da ya yi amfani da shi wanda hakan ya sa aka fitar da kulob din daga gasar.

Wadansu daga ciki sun nuna watakila da tsohon koci Jose Mourinho ne yake jan ragamar kulob din da kulob din Barcelona bai wulakanta su ba.

A halin yanzu  kulob din United yana cikin tsaka-mai-wuya don alamu sun nuna zai tashi a tutar babu a kakar wasa ta bana bayan ya rasa damar lashe kowane irin kofi.  Hasali ma yanzu kulob din yana kokarin gamawa ne a matsayi na hudu a gasar Firimiya ta Ingila in ba haka ba sai dai ya buga gasar Europa maimakon ta Zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa.