✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Firaminista: Mutum 9 da za su iya maye gurbin Boris Johnson a Birtaniya

Wadannan su ne mutanen da ake harsashen za su maye gurbinsa

Rahotannai daga Birtaniya sun ce Firaministan kasar, Boris Johnson, ya amince ya yi murabus daga mukaminsa wanda hakan ya kawo karshen shekaru biyu da rabin da ya yi a kan karaga.

Abu na gaba shi ne, ‘yan kasar su lalubo wanda suke ganin zai fi dacewa ya maye gurbin Johnson din su zabe shi.

Ga dai jerin wasu mutum tara da Aminiya ta kalato da ake ganin kowanne daga ciki zai iya maye gurbin Firaministan:

  • Liz Truss

Ita ce Sakatariyar Harkokin Wajen Birtaniya wadda ke da goyon bayan jam’iyyar Conservative mai mulki.

An ji Truss, ‘yar shekara 46, na cewa ranar Litinin din da ta gabata, tana goyon bayan Johnson 100 bisa 100, sannan ta yi kira ga abokan huldarta da su ma su mara masa baya.

  • Jeremy Hunt

Shi ne tsohon Sakataren Harkokin Wajen kasar, wanda kuma ya zo na biyu a takarar da suka yi da Johnson a 2019.

Wasu ‘yan kasar na sa ran dan shekara 55 din zai yi shugabanci mara kwamacala idan ya maye gurbin Johnson.

Domin kuwa, ya samu yabo a wasu ayyukan da ya jagoranta a gwamnatin Johnson. Kuma a farkon wannan shekara aka ji shi ya ce, yana da burin zama Firaminista.

  • Ben Wallace

Shi ne ministan tsaron kasar wanda a ‘yan watannin da suka gabata ya samu tagomashi a cikin gwamnati da ma jam’iyyarsa ta Conservative.

Mai shekara 55 kuma tsohon soja wanda ya taka rawa wajen damke wani dan kasar Jamhuriyar Irish da ya yi yinkurin kai hari wa sojojin Birtaniya a 1992. Ya soma harkar siyasa ne a 1999.

  • Rishi Sunak

Shi ne tsohon ministan kasar wanda ya yi murabus a Talatar da ta gabata, yana mai cewa kamata ya yi gwamnati ta zama tsayayya mai gudanar da harkokinta yadda ya kamata amma ba a ga akasin haka daga gare ta ba.

Duk da dai Sunak ya sha yabo wajen samar da tsre-tsaren da suka taimaka wa tattalin arzikin kasar a lokacin annobar COVID-19, a daya bangaren kuma ya sha suka kan matse hannun da jama’ar kasar suka ce ya yi wajen rabon tallafin COVI-19.

  • Sajid Javid

Shi ne ya kasance minista na farko da ya yi murabus a gwamnatin Johnson a 2020 bayan da ya zargin gwamnatin da ya yaudarar jama’a kan abin da ya sani game da zargin lalata da ake yi wa wani dan Jam’iyyar Conservative.

Iyayensa Musulman Pakistani ne, wanda ya zo na hudu a zaben kasar da aka yi a 2019 na neman maye gurbin Firaminista Theresa May.

  • Nadhim Zahawi

Shi ne wanda aka nada a matsayin sabon Ministan Kudi na kasar bayan wanda ke kai ya yi murabus.

Tarihi ya nuna Zahawi ya zo Birtaniya ne a matsayin dan gudun hijira daga Iraki tun karaminsa.

Mukamin baya-bayan da ya rike shi ne Sakataren Ilimi. Shi ma an ji shi yana cewa a makon da ya gabata, zai zama babbar dama a gare shi idan ya zama Firaministan Birtaniya.

  • Penny Mordaunt

Ita ce tsohuwar Ministar Tsaron kasar da Johnson ya tsige a lokacin da ya zama Firaminista bayan da ta nuna ra’ayin zaben abokin hamayyarsa a lokacin zabe.

Ta kasance mai goyon bayan ficewar kasar daga Tarayyar Turai. A yanzu dai ita ce karamar ministar kasuwancin kasar.

  • Tom Tugendhat

Shi ne Shugaban kwamitin kula da harkokin waje na majalisar dokokin kasar, kuma tsohon soja da ya yi yaki a Iraki da Afghanistan, tuni ya riga ya bayyana ra’ayin tsayawa takara a duk wata takarar shugabancin kasar.

  • Suella Braverman

Babbar lauya ce wadda ita ma ta nuna kwadayin shugabancin kasar. Braverman ta sha suka sosai daga wajen ‘yan uwanta lauyoyi sakamakon take wasu dokokin kasa da kasa da ta yi a bakin aiki.

Yanzu lokaci ne kadai zai tabbatar da wanda zai maye gurbin Boris Johnson a matsayin sabon Firaministan Birtaniya.