✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

G20 ta bukaci a wadata duniya da rigakafin COVID-19

Shugabannin kasashe masu karfin tattalin arziki (G20) sun bukaci sauran kasashe su tabbatar an samar da wadataccen rigakafin cutar coronavirus a ko’ina a duniya. Da…

Shugabannin kasashe masu karfin tattalin arziki (G20) sun bukaci sauran kasashe su tabbatar an samar da wadataccen rigakafin cutar coronavirus a ko’ina a duniya.

Da yake kiran, Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya ja hankalin sauran shugabannin kasashe da su bayar da tasu gudunmawar domin ganin rigakafin ya wadata a fadin duniya.

Ita ma Shugabar Jamus Angela Merkel, ta kirayi sauran shugabannin da su sanya wadattun kudade wajen samar da rigakafin cutar domin ya samu a ko’ina.

Sai dai Shugaba Trump na Amurka bai halarci taron na yaki da annobar coronavirus da inganta rayuwar jama’a bayan shudewarta ba.

An fara taron na G20 na kwana biyu ne a kasar Saudiyya ranar Asabar 21 ga watan Nuwamba, bisa jagorancin mai masaukin baki, Sarki Salaman bin Abdulazeez na Saudiyya.