✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar cin kofin duniya: Azal ta fada wa Brazil

A ranar Talatar da ta wuce ne kasar Jamus ta yi kaca-kaca da Brazil a wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya,…

A ranar Talatar da ta wuce ne kasar Jamus ta yi kaca-kaca da Brazil a wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya, inda ta lallasata da ci 7-1.
Wannan ci da Jamus ta yi wa Brazil, ba a taba yin irinsa a tarihin gasar a matakin Semi Fainal ba.
dan kwallon Jamus Thomas Muller ne ya fara zura kwallo a ragar Brazil kafin daga bisani Miroslab Klose ya kafa sabon tarihi na dan kwallon da ya fi zura kwallaye a raga a gasar bayan ya zura kwallo ta biyu kuma ta 16.  Toni Kroos ne ya zura kwallaye biyu kafin Sami Khedira ya zura kwallo ta biyar kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Jim kadan bayan an dawo hutun rabin lokaci ne dan kwallon Jamus Andre Schurrle ya zura kwallaye biyu kafin dan kwallon Brazil Oscar ya zura kwallo dayan da ta sa aka tashi wasan 7-1.
Da yawa daga cikin magoya bayan Brazil sun barke da kuka a yayin wasan saboda irin wulakancin da ’yan wasan Jamus suka yi wa na Brazil a gidansu.
Tuni kocin Brazil Scolari ya bai wa daukacin ’yan kasar hakuri a kan wannan abin kunya da suka yi a tarihin gasar yayin da shi ma Kyaftin din kungiyar Dabid Luis shi ma ya aika sakon ba magoya bayan Brazil a gasar hakuri.