✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Firimiyar Ingila: Gobe Liberpool za ta kece raini da Man United

A gobe Asabar idan Allah Ya kaimu za a yi wasa mai zafi a tsakanin kulob din Liberpool da kuma na Manchester United da ke…

A gobe Asabar idan Allah Ya kaimu za a yi wasa mai zafi a tsakanin kulob din Liberpool da kuma na Manchester United da ke Ingila a ci gaba da gasar rukunin firimiyar Ingila.  Wasan zai gudana ne a filin wasa na Liberpool da ake kira Anfield da misalin karfe 12 da rabi na rana agogon Najeriya.

Kawo yanzu Manchester United ce ta biyu a teburin gasar bayan ta hada maki 19 daga wasanni bakwai  yayin da Liberpool ta kasance ta bakwai bayan ta hada maki 12 a wasanni 7.

Tun da aka fara gasar firimiya ta bana kulob din Manchester United bai samu rashin nasara a dukkan wasannin da ya yi ba in ban da kunnen doki, don haka ake ganin wannan wasa tamkar gwajin dafi ne ga kocin United Jose Mourinho.

Sai dai Liberpool za ta iya fuskantar matsala ganin dan wasan gabanta Sadio Mane ba zai buga wasan ba saboda raunin da ya samu kuma zai shafe makonni shida yana jinya, da hakan ya sa ake ganin Manchester United za ta samu dama wajen ganin ta doke Liberppol a gida.  Amma masana harkar kwallo suna ganin harkar wasa ba haka ta gada ba, don dan hakin da ka raina shi ke tsole maka ido, don haka akwai yiwuwa Liberpool ta ba marada kunya duk da rashin dan kwallon gabanta Sadio Mane a wasan.