✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gida ya rushe ya kashe mutum uku a Agege

A safiyar Asabar din da ta gabata ce al’ummar Unguwar Abeje da ke daura da Unguwar Markas a Agege, Legas suka wayigari da rushewar sashen…

A safiyar Asabar din da ta gabata ce al’ummar Unguwar Abeje da ke daura da Unguwar Markas a Agege, Legas suka wayigari da rushewar sashen wani gidan haya da mutum kusan dari ke zaune a ciki abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum uku.

Wata mace mai suna Maimunatu Ibrahim da ke zaune a gidan tare da ’ya’yanta uku da mahaifiyarta ta shaida wa Aminiya cewa a safiyar ranar da lamarin zai auku ginin ya nuna alamu sosai, ta ce masu gidan sun zo da magina wadanda suka tabbatar musu ginin zai rufta, “Muna cikin daki sai muka ji ’ya’yan mai gidan sun zo suna cewa mu gyara nan, mu gyara can, a haka ana cikin magana sai muka ga bulo ya fado daga nan sai kasa ta fara zubowa kafin ka ce kwabo sashen gidan ya rufto, saShen bene ne ya rufta kan ban daki da dakin girki da ke cikin tsakar gidan, akwai matar da take wanke-wanke a wurin da danta da kuma yarinya ’yar shekara 11 da abin ya rutsa da su suka rasu,” inji ta.

Ta ce da lamarin ya faru sai suka ruga suka nufi daki kafin daga bisa ni suka fice daga gidan.   Malam Auwwalu dorayi Babba da shi ma yake zaune a gidan ya shaida wa Aminiya cewa akalla akwai magidanta 25 da ke haya a gidan kuma kowannensu na da ’ya’ya da mata inda ake da sama da mutum dari da ke rayuwa a gidan. Ya ce sakaci tare da kaddara ne suka kai ga aukuwar lamarin. “In ka duba ko masallacin da ke gabanmu mai bene biyu shi ma a tsage yake amna haka mutane suke shiga suna yin Sallah, ai ka ga mu bakaken fata muna da sakaci, yanzu in ka lura za ka ga wadanda wannan lamari ya shafa talakawa ne, gwamanati ta ba mu wa’adin awa uku mu tattara namu mu bar gidan amma ba ta ba mu tallafin ko kwabo ba, to a ina suke so mu saka kanmu? Legas ce fa? Idan kana so ka kama hayar daki daya kacal sai ka tanadi akalla Naira dubu 170, to mu wannan abu ya same mu babu shiri bagatatan ya zo mana to ina za mu saka kanmu?” inji shi.

A cewar Shugaban Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Legas Mista Adesina Tiamiyu tuni aka fitar da mazauna  gidan.  Ya ce hukumarsu ta samu labarin aukuwar lamarin da ranar Asabar da misalin karfe 10 da minti 48.  Ya ce hukumar ta kai daukin gaggawa tare da hukumar kashe gobara da ’yan sanda da sauran al’ummar yankin, sai ya yi kira ga jama’a su rika lura da gidajen da suke zaune in sun ga sun tsage don su ankarar da hukuma.

A cewar mai magana da yawun Hukumar Kula da Tsarin Gina Gidaje a Legas, Uwargida Titi Ajirotutu, gidan daga gaba bai nuna alamar tsufa ko raunana ba illa kawai sashin saman benen da ke cikin gidan inda a kasansa aka yi makewayi da dakin girki, mun kulle gidan, hukumarmu na yin kokarin duba gidaje daya bayan daya domin kare sake aukuwar hakan.

Hukumar ta zana jan fenti a  wani masallaci da ke daura da gidan da ya rushen, masallacin mai bene biyu shi ma yana da tsaga ana ci gaba da gudanar da Sallah da a cikinsa. Alamar jan fenti na hukumar alama ce da ke nuni da hadarin ginin kuma hukumar za ta rushe shi.

Rushewar tsofaffin gidaje ba bakon abu ba ne a Legas inda hakan ke janyo salwantar rayuka da dukiyoyin al’umma duk da kokarin gwamnatin jihar na kare hakan domin sau tari jami’anta kan zagaya don duba gidaje inda sukan tashi mutanen da gidajensu ke da tsaga da alamun rushewa.  Gwamnatin Legas ta kuma fitar da dokar duk gidan da ya rushe da kansa ya zama mallakar gwamnatin jihar.