✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gidauniya Ta Dinka wa Marayu 103 Kayan Sallah A Gombe

An raba wa nakasassu 21 Zakka ta Naira miliyan daya

Gidauniyar Zakka Da Wakafi a Jihar Gomba ta dinka wa marayu da marasa gata 103 kayan sallah.

Gidauniyar ta kuma raba zakka Naira miliyan daya ga wasu nakasassu 22.

Da yake zantawa da wakilinmu bayan bikin yaye mata 88 da gidauniyar ta koya wa sana’oin hannu domin dogaro da kansu, shugaban gidauniyar Dakta Abdullahi Abubakar Lamido, ya ce gidauniyar ta dinka wa marayun kayan sallah ne daga irin sadaka da take samu daga jama’a.

Dokta Abdullahi Lamido ya ce da zarae sun samu kudi, gidauniyar ba ta ajiyewa, sai dai ta nemo mabukata, da yake tana da sunayensu, su sai su raba musu.

“Duk abin da ya shigowa gidauniyar da sunan sadaka ba ma ajiye shi raba shi muke yi sai dai a wasu lokuta mukan ajiye wani abu kadan saboda ko-ta-kwana dan wani abu yakan iya bijirowa daga baya” inji shi.

Shugaban ya yi kira ga masu hannu da shuni da cewa su dinga kawo gudumawarsu ga gidauniyar ana rabata ga mabukata domin yin tarayya a aikin lada.

Wasu marayu da muka zanta da su sun bayyana cewa bayan Allah wannan gidauniy ita ce gatansu domin tana share musu kwalla.