✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Goodluck Jonathan

Zabe kamar mai ciki ko juna biyu yakan kasance, musamman a yankunan da ake wa lakabi da kasashe masu tasowa, irin Najeriya. A sauran sassan…

Zabe kamar mai ciki ko juna biyu yakan kasance, musamman a yankunan da ake wa lakabi da kasashe masu tasowa, irin Najeriya. A sauran sassan duniya da kuma ake wa lakabi da wadanda sun ci gaba, nan kuma zabe kan kasance abin da aka haifa ne kai-tsaye, wato abin ya tabbata, domin tun duriyar cikin an san abin da aka kunsa a ciki da abin da ake fatar gani bayan watanni, duk da cewa a wasu sassan ana samun wabi, amma alkalumma da kididdiga sun fi komawa ga daidaituwar lissafi, ko da kuwa ba a samu haduwar komai da komai ba.

Me nake ta neman bayyanawa a nan? Abin da ya faru a tsakanin ranar Asabar zuwa yau dangane da zaben Shugaban kasa da aka yi a Najeriya shi ne yake harara ta, shi ne kuma nake son mu dan taba, mu waiwaya, domin ganin ko yadda Allah Ya taimaka muka haye ruwan da ya nemi ya cinye mu da ma kasar baki daya, yin mu ne ko wani can daban.
Tunda aka fara hada-hadar zaben da yanzu muke ta murna da sowa kan nasarar da aka samu, wasu daga cikin al’ummar kasar nan ke ta addu’a da fatar Allah Ya sa a juye lafiya, abin da za a haifa kuma ya kasance cikin koshin lafiya, iyaye da ’yan uwansa kuma su zamanto cikin walwala da jin dadi. Bisa ga dukkan alamu Allah Ya karbi addu’o’in bayinsa da suka yi ta yi na Ya kawo canji cikin ruwan sanyi da lumana. An yi zabe, an kidaya, an kuma tabbatar da zabe ba tare da tashin hankali ko kashe-kashe da tada zaune-tsaye ba.
Wannan, ni shi ne abu na farko da ya burge ni game da zaben da aka yi, musamman ganin rawar da Shugaba Goodluck Jonathan ya taka wajen ganin komai ya tafi daidai. Na san wani zai iya cewa wace rawa ya taka, bayan ba yadda zai yi ne, shi ya sa?
Idan muka koma cikin tarihi za mu iya fahimtar irin rawar da ya taka ko da kuwa ba ita ya so ya taka ba, amma Allah Ya juye lamarin. A zamanin Jamhuriya ta Farko, duk fadi-fadi tashi da hargidibalen da ya dabaibaye zabe da siyasar wancan lokaci tana da alaka da hannun hukuma dumu-dumu a ciki. A tarayyar Najeriya da badakalar zaben lardunan Arewa da Yamma da Gabas daga baya kuma, Kudu-maso-Yamma, sun ta’azzara ne daga irin son zuciya da nuna ko-in-kula da aka yi wa jam’iyyun adawa da neman murde zabe ta kowace irin fuska. Haka abin ya kasance a Jamhurriya ta Biyu, ba a bar jama’a da kuri’unsu sun yi amfani ba, shi ya sa ko da sojoji suka kunno kai ba abin da al’ummar kasar suka yi face, murna da sowa. Ke nan, duk ta inda aka bullo al’ummar ce ke tagayyara, tsarin ci gaba ne ke shan wahala, domin kuwa duk da rashin kyawon mulkin dimokuradiyya, mulkin soja komai ingancinsa, lalatacce kuma mummuna ne. Amma da yake abin ya kasance abin nan da Hausawa ke cewa, wanda ya fada rijiya in ka mika masa takobi kamawa zai yi, shi ne kadai dalilin da ya sa aka rungumi soja.
Da kuma sojan ya zo ya yi watsi da tsarin dimokuradiyya, ya yi watangaririya da jam’iyyun siyasar, ya rushe na rushewa, ya kuma kafa na kafawa, daga baya ya yi zabe, ya kuma rushe zaben, me muka fahimta dangane da haka? Gaskiya daya ce, in ana son a bar tsari ya inganta masu kula da shi, su ne masu yin haka.
Saboda haka barin a yi zaben yadda ya dace, ci gaba ne, kuma Shugaba Goodluck ya tabbatar da haka, ya cancanci yabo. In da ya so, ba zai bari irin su Jega su matso kusa da kujerar shugabancin hukumar zaben ba! In da ya so da bai ba hukumar kudaden da take bukata domin ta gudanar da kyakkyawan zaben ba! In da ya so da bai bari an yi amfani kadi-rida ba, balle har a samu damar gudanar da zabe nagartacce ba! In da ya so da ya turo sojoji zuwa cikin rumfunan zabe domin su yi yadda yake so! In da ya so da bai bari an yi zaben ba, sai ya yi kutu-kutun da komai zai sukurkuce don kada a samu nasarar zabe!
Ke nan abin da ke da muhimmanci shi ne mu bayyana cewa barin a yi zaben yadda ya dace, wani bangare ne na samar da zaman lafiya a Najeriya, kuma Shugaba Goodluck ya taka muhimmiyar rawa a nan. Ba wannan ba kadai, yadda abubuwa suka nemi su sukurkuce a lokacin bayyana sakamakon zaben, in da Shugaba Jonathan ya so, kuma niyyarsa ita ce ya tabbata a mulki da tuni ba murna muke yi ba yanzu, kila sai tarzoma, wannan wutar ma an kashe ta da gudunmuwarsa.
Abu na karshe shi ne yadda ya amince da sakamakon zaben da ba a kammala hada shi ba, ganin cewa wannan shi ne daidai domin mayar da Najeriya bisa turbar da ta dace, a kuma kauce wa zubar da jini. Nan ma ya sanya hannu domin daidaita lamurra. In da ya so da ya yi irin ta tsohon Shugaban kasa Babangida, da ya hango abin da ba ya so zai faru a zaben da ya shirya, ai rushe komai da komai ya yi, ya ce in ta fanjama, fanjam! Kuma an fanjamar, domin rayukan da aka rasa ba sa kidanyuwa!
Daga karshe godiya duka ga Allah take da Ya saita tunaninmu duka, Ya kuma sa fahimta da tsinkaya da sanin ya kamata a zukatan shugabanni da mabiyansu ta yadda muka yi zabe lami lafiya, aka bayyana sakamako lami lafiya, Jonathan ya burge da ya yarda da yin Allah ya kira wanda ya ci ya taya shi murna.
Fatarmu ita ce mu harari gaba! Ta Jonathan ta wuce, yanzu sai Buhari da neman kawo gyara. Wace gudunmuwa za mu iya bayarwa a nan?
Za mu dora insha Allah