✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Goyon bayan Atiku: Mama ta raba APC a Taraba

Goyon bayan da Ministar Harkokin Mata Hajiya A’isha Jummai Alhassan ta nuna wa tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya jawo wa Jam’iyyar APC baraka…

Goyon bayan da Ministar Harkokin Mata Hajiya A’isha Jummai Alhassan ta nuna wa tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya jawo wa Jam’iyyar APC baraka a Jihar Taraba, inda wadansu magoya bayan jam’iyyar suka juya wa Jummai Alhassan din baya.

Kafin Hajiya Jummai Alhassan wadda ake kira da Maman Taraba ta nuna goyon baya ga tsohon Mataimakin Shugaban kasar, wadansu daga cikin gaggan ’ya’yan Jam’iyyar APC sun juya mata baya saboda abin da suka kira kane-kane da mallake harkokin jam’iyyar a jihar.

Wadansu daga cikin manyan jam’iyyar sun kaddamar da wata kungiya mai suna kungiyar  Masu Mutunci na  Jam’iyyar APC, (Taraba APC Integrity Group)  a karkashin shugabancin tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Uba Maigari.

Wannan kungiya tana adawa da yadda Maman Taraba ta kasance sai abin da dace a jam’iyyar ake yi. kungiyar kuma ta nuna rashin amincewa da yadda shugabanin jam’iyyar ke gudanar da harkokin jam’iyyar tare da zargin cewa sun kasance ’yan amshin shatan Maman Taraba sai abin da ta ce suke yi.

Wannan kungiya da ke adawa da Maman Taraba da shugabannin jam’iyyar ta APC tana karkashin shugabancin tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Uba Mairiga sai kuma Mista Aaron Artimas wani babban dan jarida a matsayin Sakataren kungiyar.

Manyan ’ya’yan kungiyar sun hada da tsohon Mukaddashin Gwamnan Jihar Alhaji Garba Umar ‘UTC’ da Alhaji Ahmed Yusuf wanda ya taba  rike mukamin Kwamishinan Kudi na jihar, kuma ya yi takarar Gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar CPC. Sai tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Ibrahim El-Sudi wanda tsohon dan Majalisar Tarayya ne da tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar, Mista Garbey Yawe.

Akwai kuma tsoffafin sanatocin da suka hada da Sanata Abubakar Umar Tutare wanda ya taba yin Kwamishinan Kudi da Sakataren Gwamnatin Jihar da Sanata Jeol Ikenya wanda ya taba yin takarar Gwamnan Jihar da Mista Dabid Kente wanda shi ma ya taba yin  takaranr Gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar SDP.

Sauran ’yan kungiyar sun hada da tsofaffin shugabannin majalisar jihar su uku da suka hada da Alhaji Habu Isa Ajiya da Alhaji Hamidu Mayorenewo da Ibrahim Dokta, sai kuma tsofaffin shugabannin kananan hukumomi da tsofaffin ’yan majalisa da tsofaffin manyan sakatarori da sauran manyan ’ya’yan jam’iyyar.

Da yake jawabi ga manema labarai Sakataren kungiyar, Mista Aaron Artimas ya ce sun kafa kungiyar ce a karkashin Jam’iyyar APC don samar wa jam’iyyar mutunci da kuma jama’a.

Ya ce bukatarsu ita ce su karbe mulki daga hannun Jam’iyyar PDP domin ciyar da jihar gaba. Sakataren ya ce wannan kungiya ba an kafa ta a matsayi kishiya ga shugabanin jam’iyyar ba ne, domin suna biyayya ga jam’iyya illa kawai ba su yarda da yadda ake tafiyar da jam’iyyar ba ce a jihar.

Sakataren ya ce jam’iyyar ba ta mutum daya ba ne, kuma dole ne a bai wa duk dan jam’iyya dukan dama ba a ware wani ko wata a ce ita ce kawai ke da iko wadansu ba su da dama ba. Ya ce manufarsu ita ce a nuna adalci ga dukan ’ya’yan jam’iyyar.

Ya ce kalaman da Sanata Jummai Alhassan ta yi na cewa za ta mara wa tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar baya a zaben shekarar 2019, sun nuna a fili cewa ba ta tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari. 

Mista Artimas ya ce haka ma shugabanin Jam’iyyar APC na jihar su ma ba sa tare da  Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin tare da Sanata Jummai suka tafi gidan Atiku Abubakar kuma suna nan zaune Sanata Jummai ta yi wadanan kalamai.

Mista Aaron Artimas ya kara da cewa Sanata Jummai ba ta mutunta duk wani dan Jam’iyyar APC  sa’annan ta kasance mai girman kai da isgilanci ga ’ya’yan jam’iyyar. 

“Kuma cewa wai ta kashe wa jam’iyyar kudi, wannan maganar banza ce domin sauran ’ya’yan jam’iyyar suna taimaka wa jam’iyyar da kudade da kayan aiki kamar yadda ya kamata,” inji shi.

Ya ce in maganar cewa tana kashe wa jam’iyyar kudi gaskiya ce, Jam’iyyar APC ba ta da ofisoshi masu kyau a kananan hukumomin jihar kuma ba inda jam’iyyar ke da motar hawa a dukan kananan hukumomin jihar.

Sakataren ya ce ofinshin jam’iyyar na jihar ba ya da wadattaun kayan aiki kuma shi ne koma-baya a dukan ofisoshin jam’iyyar da ke fadin kasar nan. “Ga dukan alamu Sanata ba ta tare da Shugaba Buhari wanda shi ne wanda ya ba ta wannan mukamin Minista da take tinkaho da shi har ma tana yi wa shi kansa Shugaba Buhari rashin kunya,” inji shi.

Sakataren ya ce kungiyar tana bai wa Sanata Jummai shawara ta ajiye aikinta ta koma wajen uban dakinta Atiku Abubakar domin ta kasance mara da’a da biyayya kuma mai cin amana.

 

PDP ta ji dadi 

Bincikin da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa bangaren gwamnatin jihar na Jam’iyyar PDP ya ji dadin barakar da aka samu da kuma tsaka-mai-wuya da Sanata Jummai Alhassan ta samu kanta a ciki, domin dama ta kasance masa kadangaren bakin tulu.

Wani  babban jami’in gwamnatin Jihar Taraba wanda bai son a bayyana sunansa, ya ce Sanata Jummai ta kasance mace ’yar siyasa wadda ba ta tsoron kowa kuma ba ta tsoron kashe kudinta a fagen siyasa, kuma wadda gwamnatin jihar ta dauke wata babbar barazana ga burin Gwamna Darius Ishaku na yin tazarce a shekarar 2019.

Jami’in ya ce a zaben shekarar 2015, Sanata Jummai Alhassan ta ba su wahala, kuma da ba su yi da gaske ba, da ta ba su kunya.

A cewarsa da wuya a samu wani daga cikin ’ya’yan Jamiyyar APC a jihar, wanda zai iya taka rawa ta fuskar siyasa kamar yadda Sanata Jummai ta yi.

Sai dai kalaman na bangaren Gwamnatin Jihar sun sha bamban da na wadansu gaggan ’ya’yan Jam’iyyar APC wadanda suke adawa da Sanata Jummai Alhassan.

A cewar Alhaji Ahmed Yusuf, maganar cewa Sanata Jummai ce kawai mutanen gwamnatin jihar ke tsoro ba gaskiya ba ce, domin dukan wadanda suke cikin wannan bangare na Jam’iyyar APC kowa ya san ba kanwar lasa ba ne domin da su aka fara siyasar jihar kuma sun taka muhimmiyar rawa.

Ya ce ba wanda zai gan su ya ce su ba ’yan siyasa na kwarai ba ne, “Dukanmu muna da magoya baya a dukan sassan jihar kuma mun kasance mun rike mukamai daban-daban a jihar da Gwamnatin Tarayya a lokuta daban-daban.

Alhaji Ahmed Yusuf, ya ce abin kunya ne ma Sanata Jummai ta ce tana kashe wa Jam’iyyar APC kudi fiye da kowa, amma ofisoshin jam’iyyar na jiha da kananan hukumomi ba su da ko motar hawa.

Ya ce shi kansa a cikin mako biyu kacal ya taimaka wa jam’iyyarsu da sama da Naira dubu 800. Haka sauran ’ya’yan jam’iyyar kowa na iyakar nasa kokarin ta fuskar taimakawa da kudade.

Shugaban Jam’iyyar APC ta Jihar, Alhaji Sani Chul ya bayyana cewa kowa ya san irin kokarin da Sanata Jummai ta yi ta fuskar rike jam’iyyar da samar da kudaden gudanar da ayyukan jam’iyyar yau fiye da shekara uku.

Shugaban ya ce dukan masu wadannan maganganu suna yi ne don son kansu kuma a Jihar Taraba kowa ya san cewa Sanata Jummai ita ce ta rike Jam’iyyar APC.

Da wakilinmu ya tuntubi Sanata Jummai Alhassan ta waya ta ce tana nan a cikin Jam’iyyar APC, kuma ba gudu ba ja da baya. Sai dai  ta ki yarda ta amsa wasu tambayoyi domin a cewarta ta yi maganganu masu yawa a ka wannan batu.