✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gurgu dan Najeriya ya yi sabuwar bajinta ta duniya a wasan daga nauyi

dan Najeriya mai suna Yakubu Adesokan ya kafa sabon tarihi na duniya a gasar daga nauyi a wurin Gasar Wasanni ta Afirka da ake gudanarwa…

dan Najeriya mai suna Yakubu Adesokan ya kafa sabon tarihi na duniya a gasar daga nauyi a wurin Gasar Wasanni ta Afirka da ake gudanarwa a Kongo.
Adesokan, wanda a baya ya rika ciwo wa Najeriya lambobin yabo a gasannin na duniya ya kafa sabon tarihi ne a ajin maza na kilo 49 inda ya daga karfe mai nauyin kilo 182 da rabi ya lashe wa Najeriya lambar zinare a gasar.
Wani abin mamaki shi ne kafin tafiya Kongo, Adesokan ya ce, ya ma riga ya ci wa Najeriya lambar zinare a tunaninsa, amma abin da yake fata ya lashe lambar da gagarumar nasarar da zai kafa sabon tarihi a duniya.
“Burina in yi wata bajinta a bana, wadda za ta kara daukaka matsayina a duniya tare da gabatar da ni a matsayin daya daga cikin karfafan ’yan wasan motsa jiki da za a kalla a gasar wasan Olamfik na nakasassu da za a gudanar a Rio a shekarar 2016 da aka sanya wa suna ‘Rio 2016 Paralympic Games’,”inji shi.
Adesokan ya shaida wa kafar labarai ta paralympic.org  kafin a fara gasar a Kongo cewa nakasassu da dama musamman masu daga nauyi za su samo wa Najeriyalambobin zinare da dama kuma sai ga shi sun fara da kafar dama inda Adesokan ya kafa tarihi.
Kimanin ’yan wasa 100 daga kasashen Nahiyar Afirka 20 ne za su fafata a wasan daga nauyi a wani banagre na gasar ta kasashen Afirka.