✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwajin DNA ba zai tabbatar ko ya kore nasaba ba — Malamai

Gwaji ne da ake yi don tantance asali wajen tabbatarwa ko kore nasaba.

Gwajin kwayoyin halitta na DNA abu ne da ya game duniya a wannan zamani, musamman a kasashen da suka ci gaba.

Gwaji ne da ake yi don tantance asalin wanda aka yi wa inda suke amfani da shi wajen tabbatarwa ko kore nasaba.

Sai dai ko a kasashen da suke amfani da gwajin wasu lokuta akan samu matsala.

Misali a wani shirin Taba-Kidi-Taba-Karatu na BBC Landan an taba bayar da labarin wata takaddama a tsakanin wani magidanci da wani kwarton matarsa wanda baya matar mutumin ta samu ciki kuma an tabbatar tagwaye take dauke da su, sai kwarton ya ce duk yadda za a yi daya daga cikin ’ya’yan nasa ne, kuma a karshe da aka yi gwajin DNA din sai ga shi ya nuna cewa lallai dan nasa ne.

Aminiya ta tuntubi malamai magada don sanin matsayin addini a kan sakamakon irin gwaji tare da sanin ko ana iya amfani da sakamakon gwajin wajen tabbatarwa ko kore nasabar da daga mahaifinsa.

Fitaccen malamin addinin Musulunci a birnin Kano, Sheikh Umar Sani Fagge ya shaida wa Aminiya cewa shi gwajin DNA wani abu ne da yake kara nuna kudirar ubangiji wajen halittarSa saboda a cewarsa Allah (SWT) ba Ya maimata abu daya.

“Shi ya sa kowa yake da nasa nau’in,” inji shi, sannan ya ce ita kalmar nasaba tana samuwa ne kawai ta hanyoyi biyu, aure da mallakar baiwa, “Don haka wanda ya yi lalata da mace ta haihu, to, dansa ne na jini amma ba na nasaba ba, domin nasaba tana kawo abubuwa uku, ’yan uwantaka da gado da halacci ko haramcin aure a tsakani. Don haka, ba a aiki da sakamakon DNA wajen kore nasabar abin da aka haifa sai dai a je wajen alkali a yi Li’ani.”

Haka kuma, malamin ya ce koda gwajin DNA ya tabbatar da wata alaka a tsakanin wadansu to a shari’a babu ita sai dai in da ma akwai ta a shari’ance.

Amma Shehin Malamin ya ce za a iya amfani da sakamakon gwajin DNA don tabbatar da abin da, da ma akwai shi saboda Manzon Allah (SAW) ya amince da yin amfani da ilimin “kiyafa” wanda ilimi ne da ake duba tafin hannu ko kafafu don gane dangin mutum.

Shi ma a nasa bangaren, Farfesa Ahmad Murtala, wanda Shehun Malamin Musulunci ne, kuma Shugaban Sashin Nazarin Addinin Musulunci da Shari’ar Musulunci na Jami’ar Bayero ta Kano ya bayyana cewa amfani da wani bangare na jikin dan Adam don tabbatar da asalin mutum ba sabon abu ba ne a Musulunci, domin kuwa tun kafin Musulunci Larabawa suna da masu irin wannan ilimin, kamar yadda Ahlu Mudrij bin Murrah daga kabilar Banu Kinanah suka shahara da haka.

Sai dai ya ce, “A asalin shari’a ba za a yi amfani da sakamakon gwajin DNA wajen tabbatarwa ko kore da ba. Saboda ayoyi da hadisai sun riga sun yi bayanin hujjojin da ake aiki da su wajen tabbatar ko kore nasaba.”

Malamin ya ce duk matar da ta yi wata shida da aure, to duk abin da ta haifa na mijinta ne idan kuma yana so ya kore hakan, to, sai dai a yi Li’ani a kotu, ba DNA ba. Saboda fadin Manzon Allah (SAW) “Dan da aka haifa na mai shimfida ne” wato mijinta.

Ya kara da cewa shari’a ta yi haka ne don hana tozarta dan Adam.

Amma a cewarsa za a iya aiki da gwajin DNA a wasu al’amura na daban, kamar tantance nasabar mutum bayan an yi gobara ko hadari ko bata, da aka kasa gane ko wane ne shi.

Amma ba za a yi aiki da shi ba wajen gano barawo ko wanda ya yi kisa ba don a zartar musu da hukunci, saboda fadin Manzon Allah (SAW) “Ku kautar da zartar da hukunci idan akwai kokwanto.”

Shi ma Shugaban Sashin Nazarin Addinin Musulunci na Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano, Dokta Isma’il Muhammad Salis ya ce Shar’iar Musulunci ba a daskare take ba don haka kowane sabon abu da ya faru, wajibi ne malamai masana su hadu domin samar masa da hukunci ta hanyar kallon wannan mas’alar ta mahangar shari’a, bisa la’akari da manufofin shari’ar Musulunci (Makasidus Shari’ah).

Haka kuma ya ba da misalin irin wadannan sababbin al’amura, kamar dashen zuciyar biri ga dan Adam ko Sallar Musulmi a duniyar wata da sauransu.

“Don haka DNA ma ya fada cikin wadannan abubuwa da ake kiran su dawari’u kuma malamai sun zauna sun tattauna a kai, a inda mafi yawanci suka tafi a kan rashin halaccin dogaro da sakamakonsa don tabbatarwa ko kore nasaba a tsakanin iyaye da ’ya’ya, saboda ita nasaba tana tabbata ce ta dalilan asalin shari’a.

Ya kara da cewa duk da yake babu kuskure wajen halittar Allah da Ya bambanta tsarin halittar kowa daban da ta dan uwansa.

Amma za a iya samun kuskure a cikin hanyoyin da aka bi wajen yin gwajin. Tun daga kan na’urorin da aka yi gwajin da su, zuwa shi likitan da zai gwajin ko masu taimaka masa, zuwa mayar da alkaluman bayanai zuwa rubutu da makamantansu.Wadannan sun kara wa sakamakon gwajin DNA raunin da ba za a yi aiki da shi wajen keta alfarmar dan Adam ba a kore masa uba, bayan ga dalilan asalin shari’a.

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Gidan Gwamnatin Kano kuma malami a Kwalejin Nazarin Shar’iar Musulunci ta Kano, Dokta Mujtaba Ibrahim Ramadhan ya bayyana cewa ko a zamanin Manzon Allah (SAW)akwai wani abu mai kama da haka, saboda an samu lokacin da sahabinsa Muhriz al-Mudliji ya shiga ya samu wadansu mutum biyu sun lulluba suna barci amma kafafuwansu sun fito waje, sai ya ce ai kuwa wadannan kafafun asalinsu daya ne, kuma haka ne saboda Zaidu bin Harisa ne da dansa Usama bin Zaid suke kwance.

Kuma Manzon Allah (SAW) ya yi farin ciki da wannan ilimi da Muhriz ya yi amfani da shi.

Amma a cewarsa mayar da hankali wajen yin gwajin DNA ga ma’aurata yana iya haifar da matsaloli masu yawa a cikin al’umma.

Kuma ya ba da misali da wata hira da aka yi da wani mai gwajin DNA a Legas da ta karade kafafen watsa labarai a kwanakin baya, inda likitan ya ba da labarin wadansu ma’aurata da ya yi wa gwajin DNA kuma sakamakon ya tabbatar da cewa ba mijin ne uban dan ba, ita kuma matar ta dage cewa ba ta taba mu’amala da wani namiji ba sai mijinta.

Da likitan ya ga sabanin ya yi karfi a tsakaninsu sai ya ba su shawara cewa ita ma matar a yi mata gwajin, ko da aka yi sai sakamakon ya nuna ita ma ba uwarsa ba ce, abin da ya nuna yiwuwar ko dai an musanya mata dan a asibitin da ta haihu, ko kuma ta yaudari mijin ne ta samo jariri ta ce ita ta haife shi.

Wannan ya nuna idan ba a lura sosai ba gwajin DNA zai iya dora laifi ga mara laifi ko ya hargitsa gidan aure ba gaira ba dalili.

Don haka, ya ba da shawara a takaita wannan gwaji ga abubuwan da suka zama larura.