✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamanti ba ta taba ba mu takin zamani kyauta ba -Umaru Sarkin Fawa

Wani mutum mai suna Muhammadu Umaru da ake yi wa lakabi da Sarkin Fawa da ke zaune a kasuwar Mil 12 a Legas ya ce…

Malam Muhammadu Umaru, Sarkin FawaWani mutum mai suna Muhammadu Umaru da ake yi wa lakabi da Sarkin Fawa da ke zaune a kasuwar Mil 12 a Legas ya ce akwai manoma da yawa da ba su taba samun takin zamani ba duk da ikirarin da gwamnati take yi na raba takin zamani kyauta ga manoma.
Malam Muhammadu Umaru, dan asalin garin Yabo da ke Jihar Sakkwato ya bayyana wa Aminiya, a wata tattaunawa, cewa bai taba samun takin zamanin gwamnati ba.
Ya ce, “Akwai manoma da yawa da ba su taba samun takin zamani ba a kauyukan Sakkwato. Misali, ni kaina a matsayina na manomi, ban taba samun takin zamanin gwamnati ba, sai dai na sa kudina na saya. Za ka ga an hada manoma biyar a kan buhu daya na taki, amma sai a fito ana fada wa duniya cewa gwamnati na raba takin zamani kyauta ga manoma. Ko bashin taki ba za ka samu ba balantana kyauta. Ka ga wannan rashin adalci ne”.
Ya ci gaba da cewa, “Babu abin da gwamnati za ta yi wa talakan kasar nan wanda ya wuce ta taimaka masa a noman da yake yi. Ga shi ba mu da hanyoyi, babu magunguna a asibitoci. Gaskiya ya kamata shugabanninmu su rika yi mana adalci”.
Umaru, wanda yake fataucin doya a kasuwar Mil 12, ya bayyana cewa har yanzu ba a yi musu wata hanya ta a zo-a-gani ba a titin kauyensu na Bungaje. “Muna kira ga shugabanninmu su rika yi mana adalci. Su rika tunawa da mu talakawa, ba sai lokacin zabe ba. Ka ga su shugabanin kudanci, idan suka sami mukami, za ka ga suna yi wa mutanensu aiki, amma mu namu sai dai su gina kansu da iyalansu. Ka ga hakan bai dace ba. Ya kamata a ce ci gaban da ke Arewa ya fi haka”. Inji shi.