✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna a Amurka ya yi murabus kan cin zarafin mata

Shi ne Gwamna na uku da zai yi murabus sakamakon aikata abun kunya.

Gwamnan birnin New York, Andrew Cuomo ya yi murabus bayan da wani bincike ya gano shi da laifin cin zarfin mata da dama.

Sanarwar da Gwamnan ya fitar a ranar Talata ta ce, taimakon da ya fi dacewa ya bayar a yanzu shi ne ya sauka ya bai wa mahukunta damar gudanar da aikinsu.

Bayanai sun ce murabus din gwamnan zai fara aiki ne daga nan zuwa kwana 14, inda zai mika mulki ga mataimakiyarsa, Kathy Hochul wacce za ta kasance mace ta farko da za ta jagoranci Jihar New York a tarihi.

Binciken wanda Ofishin Babban Lauyan Jihar New York ya gudanar ya zargi Mista Cuomo mai shekara 63 da cin zarafin mata 11, lamarin da har yanzu ya musanta.

Mista Cuomo dai ya rika fuskantar matsin lamba daga ’yan jam’iyyar Democrats bayan fitar da rahoton zarginsa da cin zarafin mata.

Daga cikin masu matsin lambar har da Shugaba Joe Biden, Shugabar Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosy da kuma Shugaban Majalisar Dattijai, Chuck Schumer.

Mista Cuomo dai shi ne Gwamnan New York na uku a jere cikin shekaru 13 da zai yi murabus sakamakon aikata abin kunya.