✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati a kula da yankunan karkara

Editan Aminiya ka ba ni dama in bai wa Shugaban kasarmu shawara game da gyaran yankunan karkara. Hakika yankunan karkara na cikin wani hali na…

Editan Aminiya ka ba ni dama in bai wa Shugaban kasarmu shawara game da gyaran yankunan karkara. Hakika yankunan karkara na cikin wani hali na bukatar gyara, musamman abubuwan da suka shafi tallafin noma da gyaran hanyoyi da kula da lafiyar al’umma. Babu abin da mutumin karkara ke bukata irin tallafin noma da kiwo da kuma koyar da matasa sana’o’in da za su rika yi a lokacin rani. Sannan akwai bukatar a yi asibitoci da za su rika karbar haihuwa, ta yadda ba sai an je birni ba, musamman a yankunan da ba su da hanyar ababen hawa da za ta fito da mutum daga kauye. Idan Gwamnatin Jam’iyyar APC a karkashin Shugaba Muhammadu Buhari ta kawo wa mutanen karkara dauki, tabbas za a rage yawan kwararar matasa zuwa birane neman abin da babu, har ta kai ga a karshe wasu sun zama ’yan bariki, kuma ba sa iya komawa karkararsu ta asali. Lallai akwai bukatar a duba wannan lamari. Domin wannan zai taimaka wa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen kawar da rashawa da cin hanci da satar dukiyar al’umma. Daga Alhaji Isyaku dan Hadeja 08023122946

Ta’aziyyar Zanna
Innalillahi  wa’inna  ilaihir  raju’un. A   madadin  ‘yan  uwa  da  iyalan Marigayi  Alhaji  Zanna  Umar  Mustapha,  mataimakin  Gwamnan  Jihar Borno  nike  mika  ta’aziyata  da fatan  Allah  ya jikansa  da  rahama Amin Daga  Garba  Sabiyola  Gashua,  Jihar  Yobe 07066581437.

Allah Ya jikan Zanna
Rai bakon Duniya, A madadin al’ummar garin Ngulde wadanda muke gudun hijira a sassan Arewacin Najeriya, muna mika sakon ta’aziyyarmu ga ‘yan uwa da iyalan mataimakin gwamnan Jihar Borno, wato ‘Alhaji Zannah Umar Mustapha’. Da fatan Allah ya jikan sa, yasa ya huta. Mu kuma da muke raye muna addu’ar Allah yasa mu yi kyakkyawan karshe. Amin summa amin.
Daga Adamu Aliyu Ngulde, dalibi A Sashein Koyon Aikin Jarida a Jami’ar Maiduguri. 08032135939, 08188020289.

Addu’a ga El-Rufa’i
Salam Editan Aminiya! Kai tsaye nake addu’ar Allah Ya sa rantsar da Kwamishinoni 12 cikin 13 da gwamnan Jahar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya yi a ranar Laraba kwalliya ta biya kudin sabulu, Allah Ya taimakemu da taimakonSa. Daga Mudassir Ibrahim Mando Jihar Kaduna 08034371602 (Facebook! Mudassir Ibrahim Mando Kaduna)

Ta’aziyyar Zanna
Hakika duk mai rai zai zama mamaci. Muryar Jama’a ta Jihar Katsina tana yin ta’aziya ga Iyalai da Gwamnatin Jihar Borno da’yan’uwa da abokan arziki na Margayi Mataimakin Gwamnan Jahar Borno.Alhaji. Zannah Umar Mustafha wanda ya rasu a makon da ya wuce. Da fatan Allah ya gafarta masa kura-kuransa yasa Aljanna ce makomar sa.Mu kuma da muke jiran namu lokaci yasa mucika da kyau da imani. Daga. ’Yan’Kungiyar Muryar Jama’a ta Jahar Katsina. 07039205659.

Ga Shugabannin Arewa
Edita ka taimake ni ka isar da sakona ga Shugabanninmu na Arewa kan wulakanci da muke gani a kan sana’armu ta acaba a Kudancin Najeriya. Rashin aikin yi ya sanya mu yin wannan sana’a. Don haka muke kira ga Gwamnatin kasar nan mai adalci ta duba lamarinmu. Daga Husaini Sunjshine Birnin Gwari, Jihar Kaduna 08032824939.

Kira ga Gwamna Ganduje
Edita a mika kirana ga Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje kan karasa aikin hanyar da ta tashi daga Hawanganji zuwa Sabon- Layi zuwa Kadafa zuwa Badari a karamar Hukumar Gwarzo. Daga Yusif Muhammad Mai hoto Sabon Layin Kara 08022518535.

Allah Ya jikan Zanna
Ina mika ta’aziyya ta ga Mai girma Gwamnan Jihar Borno Hon. Kashim Shettima da Mai Martaba Shehun Borno Alhaji Abubakar Bn Garbai Al-Amin Elkanemy da daukacin al’ummar Jihar Borno bisa rasuwar mai girma Mataimakin Gomnan Jihar Borno Alhaji Zanna Umar Mustapha a safiyar Asabar din makon jiya. Ya Allah ya jikansa da rahma Ya sa Aljanna ce makomarsa. Allah Ka sa mu cika da imani idan tamu tazo. Daga Bilya Tukur Bakori 07030225194.

Yabo ga Gwamnan Jigawa
Aminiyar Amana ku ba ni dama in yabi Maigirma Muhammad Badaru, Gwamnan Jigawa Domin yaban gwani ya zama dole. Maigirma ya yi abubuwa da dama daga rantsar da shi wadanda suka hada da:Kawo kamfanin Sukari da taimaka wa zawarawa daYa kara albashi;Ya kai Makarantar Jinya da Ungozoma Hadeja. A yanzu ya tattauna da jami’ar ABU, domin Kula da Lafiyar koda, ya kuma daukaka darajar asibitocin Hadejia da Kazaure zuwa asibitoci na musamman.Wajen Ilimi za a dauki malamai  4,500 aiki da dai sauran ayyuka na alkairi. Babana ba ka bai wa ‘yan jarida da masoyan ka kunya ba. Da fatan sauran gwamnoni za su yi koyi da kai. Daga Hansa’u Hussaini Girbobo.   08030453683.

Ga Sanata Kwankwaso
Edita ka mika min sakona ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Mu dai mutanen Jihar Kano mun samu romon dimokuradiyya ta dalilinka. Allah ne ya zaba mana maikishinmu;  muna rokon Allah Ya sa Ganduje ya yi kishin Kanawa kamar haka. Daga Yakubu Abdullahi Fulatan    / 08098686893.

A yi hakuri Katsinawa
Assalam Edita ina kira ga jama’a da su kara hakuri da wannan sabuwar gwamnti ta Jihar Katsina, Gwamna Aminu Bello Masari, bisa yadda wasu har sun fara zagin gwamna a kan ya ce ba zai biya kudin makaranta ba. A yi hakuri a ga abin da zai yi maimakon jarabawa. Daga Usaini Iliyasu Charanci 08065224569.

Yabo ga Aminiya
Salam Edita ka ba ni dama in yaba wa jaridar AMINIYA mai farin jini, musamman ga ma’abota karatun Hausa hakika wannan jarida ta zama zakaran gwajin dafi a cikin jaridu, ganin yadda ake tsara abubuwa masu ma’ana a cikinta. Wani abu da yake burgeni shi ne yadda ake fitar da labari da dumi-duminsa, misali sai mu ga abu ya faru a ranar Alhamis da yamma, amma abin mamaki sai mu ga labarin ya fito a ranar Juma’a haka kuma wannan jarida ta AMINIYA tana share mana hawayanmu, musamman yadda muke rubuto bayananmu kuma ake rubutawa ba tare da karbar komai daga gare mu ba. Don haka na ga ya zama wajibi in yaba muku, tare da yi muku addu’ar Allah ya kara daukaka ku Daga Aminu Abdu Baka Noma, Sani Mainagge Kano 08028505350.