✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Buhari alheri ce ga al’ummar Najeriya – Sheikh Alhassan Sa’eedGwamnatin Buhari alheri ce ga al’ummar Najeriya – Sheikh Alhassan Sa’eedGwamnatin Buhari alheri ce ga al’ummar Najeriya – Sheikh Alhassan Sa’eedGwamnatin Buhari alheri ce ga al’ummar

Fitatcen malamin addinin Musuluncin nan da ke Jos a Jihar Filato, kuma jigo a bungiyar Jama’atu Izalatil Badi’ah Wa Ibamatis Sunnah ta basa, Sheikh Alhassan…

Fitatcen malamin addinin Musuluncin nan da ke Jos a Jihar Filato, kuma jigo a bungiyar Jama’atu Izalatil Badi’ah Wa Ibamatis Sunnah ta basa, Sheikh Alhassan Sa’eed Adam Jos, ya ce gwamnatin Shugaban basa Muhammad Buhari alheri ce ga al’ummar Najeriya.
Sheikh Alhassan Sa’eed Adam ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, inda ya ce wannan gwamnati ta Buhari tana bunshe da alheri kuma tana nufin al’ummar Najeriya da alheri.
“Wanda duk zai yi wa Najeriya adalci ya san cewa ta karye. Tun da ta karye dole a dora ta, don haka dole ne ’yan Najeriya su ji ciwo wajen wannan dori da ake yi mata. A baya ta ko’ina an wawushe kudin Najeriya ta zama babu komai. Muna cikin wannan hali ne Allah Ya kawo wa talakawan Najeriya canjin da suke nema ta hanyar zuwan Shugaban basa Muhammadu Buhari. Don haka ina robon talakawan Najeriya mu yi haburi kan wannan canji da Allah Ya kawo mana, mu ci gaba da yi wa wannan gwamnati addu’a,” inji Malamin.
Sheikh Alhassan Sa’eed ya ce duk masu la’antar wannan gwamnati kamar suna la’antar kansu ne, domin idan gwamnatin ta lalace ba mu san inda za mu shiga ba. Don haka mu ci gaba da yi wa gwamnatin nan addu’a ta samu ta bwato dukkan kudin da aka sace ta yi wa ’yan Nijeriya aiki da su. Sai ya yi kira ga Shugaban basa ya yi duk abin da zai yi ya sassauta wa ’yan Nijeriya halin buncin rayuwar da suke ciki.