✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Filato ba ta ba Musulmi ragunan layya ba –Shugaban Izala

Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bad’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Jihar Filato Alhaji Iliya Wishishi ya ce maganar da ake cewa wai gwamnatin jihar ta sayo…

Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bad’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Jihar Filato Alhaji Iliya Wishishi ya ce maganar da ake cewa wai gwamnatin jihar ta sayo raguna da shinkafa na Naira miliyan 42 ta raba wa al’ummar Musulmin jihar ba gaskiya ba ce.
Alhaji Iliya Wushishi ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce a matsayinsa na shugaban kungiyar Izala ba a ba su ba kuma ba su ga wanda aka ba shi ba. Ya ce idan ma gwamnatin Filato ta ware kudade ta sayi raguna da shinkafa to kwamitin da ta damka wa alhakin raba su bai raba ba, sai dai in sun raba wa yaransu da ’yan uwansu ne kawai.
Alhaji Iliya Wushishi ya ce haka aka yi a watan azumin da ya gabata, inda aka ce gwamnatin jihar ta ware sama da Naira miliyan 40 ta sayo shinkafa da gero don raba wa Musulmi amma ba raba musu ba.
Ya ce ya kamata gwamnatin jihar ta san cewa idan har tana ware wadannan kudade ne don tallafa wa al’ummar Musulmi, to ba sa zuwa hannun al’ummar Musulmin da aka bayar da dominsu, saboda wadanda ake damka wa aikin ba sa yin gaskiya.
Wakilinmu ya buga wa Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar Filato kuma Shugaban Kwamitin raba wadannan raguna da shinkafa Alhaji Idi Waziri waya, don jin ta bakinsa kan wannan al’amari amma bai dauki wayar ba. Har ila yau ya buga wa daya da cikin ’yan kwamitin kuma Mai ba Gwamnan Jihar Filato Shawara ta Musamman kan Harkokin Addinin Musulunci Barista Nasiru Goshi waya don jin ta bakinsa kan wannan al’amari shi ma bai dauki wayar ba.