✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ba ta cika alkawarin tallafa wa mabarata ba – Alaramma Tukur

Shugaban kungiyar mMalaman Allo ta Hizbur Rahim da ke Kano Alaramma Tukur Ladan ya soki kamen mabarata da gwamnatin Jihar Kano ta fara, inda ya…

Shugaban kungiyar mMalaman Allo ta Hizbur Rahim da ke Kano Alaramma Tukur Ladan ya soki kamen mabarata da gwamnatin Jihar Kano ta fara, inda ya ce kafin a fara kamen ya wajaba a cika wa mabaratan alkawarin tallafa musu da gwamnatin ta yi.
Alaramma Tukur Ladan ya bayyana haka ne a hirarsa da Aminiya, inda ya ce “Ina yaba wa gwamnatin kan hana bara, sai dai ba na goyon bayan kame almajirai da ake yi alhali ba ta cika alkawuran da ta yi na kula ko ba da tallafi gare su ba.”
Alaramman ya ce an kira alarammomi da shugabannin nakasassu, inda gwamnati ta tambayi kowa aiki ko sana’ar da zai iya, kuma ta ce za ta tallafa musu da kudi don jan jari. Ya ce amma yanzu haka ba a ba almajiran tallafin ba aka fara kama su. “Da a ce gwamnati ta ba da tallafin, duk wanda ta kama yana bara ta yi daidai,” in ji shi.
Alaramma Tukur ya ce laifin shugabannin baya da sakacinsu ya jawo ake yin bara, domin ya ce tun 1966 ake yin bara kullum sai a ce babu kyau, ba tare da an yi wani tanadi na taimakon mabaratan ba.
Game da tsarin taimakon almajirai na Gwamnatin Tarayya kuwa, ya ce “Da muka je Sakkwato inda ta kaddamar da tsarin makarantun allo, gini kawai muka gani kawai ba tare da an tanadi komai na rayuwar almajiran ba.”
Ya soki gwamnatoci da almubazzarantar da kudaden jihohinsu tare da raba wa ’yan wasan kwallon kafa motoci, alhalin an kyale almajirai makaranta kur’ani ba tare da wani taimako ba.
Da Aminiya ta tuntubi Kwamanda Janar na Hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce tabbas gwamnati ba ta kammala shirin tallafa wa mabaratan ba, amma an jima ana gargadin cewa dokar za ta fara aiki.
Ya ce daga cikin yunkurin ne gwamnatin ta ba masu ilimi nakasassu 45 aikin gwamnati, kuma za ta rika biyan wadanda ba za su iya sana’a ba, Naira dubu goma-goma a kowane wata, wadanda za su iya sana’a a ba su jarin Naira dubu sittin-sittin.