✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnonin APC 20 sun goyi bayan a sake zaben shugabanni

A shekaranjiya Laraba ce Gwamnonin Jam’iyyar APC 20 daga cikin 24 suka rattaba hannu a kan wata takarda da suka aike wa Shugaban kasa, wadda…

A shekaranjiya Laraba ce Gwamnonin Jam’iyyar APC 20 daga cikin 24 suka rattaba hannu a kan wata takarda da suka aike wa Shugaban kasa, wadda ta kunshi goyon bayansu ga Shugaba Muhammadu Buhari kan soke karin wa’adin shekara daya da aka yi wa shugabannin jam’iyyar, kuma suka bukaci a kafa kwamitin shiryea sabon zaben shugabannin kafin 30 ga watan Yunin bana.

Aminiya ta gano cewa gwamnonin sun rika sanya hannu daya bayan daya a takardar, bayan baram-baram da suka yi a yayin ganawarsu da Shugaban kasa a fadarsa ranar Talatar da ta gabata.

Wannan dambarwa ta kunno kai ne bayan da Shugaba Buhari ya bayyana cewa karin wa’adin da aka yi shugabannin jam’iyyar na shekara daya haramtacce ne a dokar jam’iyya da kundin tsarin mulkin Najeriya.

Shugaban Majalisar Gwamnonin Najeriya, kuma Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdulaziz Yari ya bayyana wa manema labarai wannan mataki jim kadan bayan kammala taronsu a shekarajiyr, yana mai cewa, “Bayan kammala taron da muka yi jiya (Talata), mun bar ku a cikin duhu, to amma a yau mun tashi mun ga kanun labarai  iri daban-daban a jaridu cewa wai an samu rabuwar kawuna a tsakaninmu. Wannan ba gaskiya ba ne, mun dai yi taro jiya wanda bayan taron muka shiga muka tuntubi Shugaban kasa, kuma aka daga taron zuwa yau (Laraba).

“To mun kuma tuntubi dukan gwamnoni 24 na APC, kuma duk mun amince da shawarar da Shugaba Buhari ya bayar, saboda haka kowanenmu zai bi abin da tsarin dokoki suka shimfida. Ina sanar da ku cewa dukanmu mun amince a soke karin wa’adin da aka yi wa shugabannin jam’iyya tun daga kananan hukumomi zuwa jiha da kuma tarayya.”

Shi ma Shugaban Jam’iyyar APC ta kasa, Cif John Oyegun, a ranar Talatar da ta gabata ya nada kwamitin mutum 10 a karkashin shugabancin Gwamnan Jihar Filato, Barista Simon Lalong, wanda ya dora wa aikin bayar da shawara ga Buhari a kan matakin da ya dauka.