✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajjin Bana: Ƴan Najeriya sun kashe N304 Biliyan

Alhazan Najeriya sun kashe aƙalla N304 Biliyan wurin siyan kujerun Hajjin 2023. Binciken Aminiya ya nuna cewa kujerar Hajji a hannun hukumomin jin daɗin alhazai…

Alhazan Najeriya sun kashe aƙalla N304 Biliyan wurin siyan kujerun Hajjin 2023.

Binciken Aminiya ya nuna cewa kujerar Hajji a hannun hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi ta kama ne akan N3.2 Miliyan.

Amma farashin kamfanonin ƴan kasuwa wanda ake kira jirgin yawo ya tashi ne kan N4 Miliyan a bana.

Jigilar alhazai: Saudiyya ta ba jiragen Najeriya damar yin sawu 15 a kullum

Yadda nakasassu da tsofaffi suka yi aikin Hajji bana

Adadin alhazan Najeriya a 2023 mutum 95,000 ne.

Idan aka lissafa N3.2 Miliyan sau 95,000 shi ne zai bada N304 Biliyan.

Wannan na nufin idan aka yi la’akari da waɗanda suka biya jirgin yawo adadin ya zarta haka matuƙa.

Farashin Hajji 2015 – 2023

Mahukunta dai na danganta hauhawar farashin kujerar Hajji da karyewar darajar Naira.

Hakan ya sa a kowace shekara farashin yake ci gaba da hauhawa.

Idan ana iya tunawa dai a 2015 an biya kujerar Hajji akan N650,000.

Bayan shekara guda kuma farashin ya ƙaru zuwa N720,000 a 2016.

A 2017 kuma farashin kujerar Hajji ya koma N960,000.

Sai a 2018 farashin kujerar ya cike N1 Miliyan cif.

Daga nan kuma sai ya ɗaga zuwa N1.2 Miliyan a 2019.

Maniyyata daga Najeriya basu samu zuwa Hajji ba a 2020 da 2021 saboda annobar Covid-19.

Amma bayan da aka dawo da jigilar alhazai a 2022 farashin ya yi tashin gwauron zabi zuwa N2.65 Miliyan.

A bana kuma ya zarta zuwa N3.2 Miliyan.

Cikon addini

Shi dai Hajji rukuni daga cikin rukunan Musulunci guda biyar.

Kuma ana buƙatar duk wani Musulmi ya aikata Hajji sau ɗaya a rayuwarsa.

Sai dai duk inda batun Hajji ya zo a Alƙur’ani ya na tafiya da sharaɗin “ga wanda Allah ya hore wa ikon yi.”