✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Halaka dan yaro Haidar: Muguntar ta isa mugunta!

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Maketatan sun kashe karamin yaro Haidar bayan sun sace shi, sun boye shi, bayan kuma sun nemi a biya…

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Maketatan sun kashe karamin yaro Haidar bayan sun sace shi, sun boye shi, bayan kuma sun nemi a biya su kudin fansa kuma bayan an biya su. Wannan keta ta isa ta zama mummunar mugunta!
Duka-duka fa yaron nan shekararsa hudu a duniya, amma sun kashe shi. Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Haidar, da ne ga kanen matata, Aminu Ahmad. An haife shi ne a cikin watan Oktoban 1999, sai ga shi a ranar Larabar makon jiya, marasa tausayi sun halaka shi. Ba wai kisan kawai suka yi masa ba, domin kuwa sai da suka sace shi, bayan sun nemi a biya su kudin fansa, sun yi alkawarin cewa za su sako shi da zarar an biya su. Ga shi an biya su kudin, amma ba su cika alkawari ba, suka aika da shi lahira, suka saka gawarsa cikin buhu, suka jefar da shi a wani wuri; kafin ’yan sanda su tsinto shi.
Wani abin takaicin kuma shi ne, da aka duba gawarsa, an ga alamun da suka tabbatar da cewa sun azabtar da shi kafin su kashe shi. Na farko dai, an ga alamun lahanta idanuwansa da wani makami mai kaifi. Wannan na alamta cewa babu mamaki ya gane daya ko wasu daga cikin makasan nasa. Na biyu, an ga alamun dauri a hannuwansa, ke nan sai da suka daure shi tamau sannan suka halaka shi. Duk wannan ukuba da suka yi, sun yi ta ne ga kankanen yaro, dan shekara hudu kacal a duniya – Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!
Kamar yadda al’amarin ya faru, a ranar Talatar makon jiya ce yaro Haidar ya tafi makarantar Islamiyya, wacce ba ta da nisa daga gidansu, a unguwar Na’ibawa, Kano. Bayan an tashi makaranta, yarinyar da ke raka shi gida ba ta gan shi ba. Nan take ta fara cigiya kuma maganar ke nan, an gane cewa an sace shi ne. Babu shakka an yi zargin cewa wanda duk ya sace shi, ya san yaron kuma yaron ya san shi. Idan ba haka ba, yaron da ya yi kuka ko ihu, domin ba zai amince ya bi bako ba haka nan zikau. (Wannan ke nuna cewa ya dace mu sake tsarin tafiyar da makarantunmu na Islamiyya, a rika tantance masu daukar yara idan an tashi daga makaranta, kamar dai yadda ake yi a makarantun boko).
Takaicin ya isa takaici – Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Ya Allah Ka tsine wa wadannan makasa na Haidar, barayi, marasa tausayi da imani. Allah Ka hukunta su da mummunar ukuba a nan duniya da kuma lahira. Shi kuwa marigayi Haidar, Allah Ka sanya shi ya zama daya daga cikin yaran Aljanna, wadanda ba su tsufa (wildanun mukhalladun). Ya Allah Ka ba iyayen Haidar, Aminu da Fatima da mu kanmu ’yan uwansu hakurin jure wa rashinsa. Takaicin kisan karamin yaron nan haidar da kuna – Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!
Rasa yaro, musamman ta hanyar sacewa ko bacewa babu dadi ko kadan. Ni kaina haka ta taba faruwa da ni a cikin watan Afirilun 2011, lokacin da dana dan shekara shida ya bata. Da ni da baban Haidar, Aminu muka yi ta hakilon nemansa. Mun sha wahala matuka. Ni da shi muka raba Kano duk da girmanta zuwa gida biyu, muka rika binciken wurare daban-daban muna kai cigiya ofis-ofis na ’yan sanda, Hisba, kangayen gidaje, asibitoci da sauransu. Mun yi tsammanin ko matsafa ne suka kama shi ko kuma ya gamu da hadari ko wani abu. Na san radadi da ukuba da wahalar batan yaro. Allah ka raba mu da irin wannan musifa, irin wadda ta samu marigayi Haidar. Abin ba dadi – Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!
A yanzu haka ina kirdadon irin ukubar da mahaifin Haidar, Aminu yake ciki. Babu shakka rashin Haidar babban rashi ne, musamman kasancewar shi ne da fari ga Aminu. Hausawa suna cewa babban wa magajin uba – lallai an yi rashin magaji a Haidar. – Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!
Lallai Aminu baban Haidar ya shiga jarabawa amma ina kiransa da ya tuna abin da Allah Y ace a cikin Alkur’ani mai girma (Sura ta 29, aya ta 2). Ya sani cewa masu imani ne kawai Allah ke yi wa jarabawa. Wannan abu da ya faru ga Haidar, jarabawa ce. Da kai Aminu da matarka, mahaifiyar Haidar (Fatima), sai dai ku dau hakuri. Allah Ya jikan Haidar, amin!