✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanyar Kaduna zuwa Abuja ta fi kowace hanya tsaro a Najeriya yau – El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai ya ce, a yanzu babu hanyar da ke da tsaro kamar hanyar Kaduna zuwa Abuja a kasar nan. Ya kuma…

Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai ya ce, a yanzu babu hanyar da ke da tsaro kamar hanyar Kaduna zuwa Abuja a kasar nan.

Ya kuma bayyana cewa, an kwashe watanni biyu da rabi ba’a samu labarin yin garkuwa da wani a kan wannan hanyar ba saboda matakai da gwamnati ke ci gaba da dauka.

Gwamnan ya kuma bayyana hakan ne bayan ya bude wani taro da na tsaro da aka yi a jihar a yanzu.
“Hanyar Kaduna zuwa Abuja a yanzu ta fi kowanne hanya tsaro a Najeriya a yanzu saboda jiragen sama na sojojin sama da ke aiki a wannan hanya suna samar da bayanai amma har yanzu mutane na jin tsoron bin wannan hanya.

“A yanzu kusan duk masu garkuwa da mutane da ke gefen hanyar duk an tarwatsa su ko kuma an kora su cikin jeji,” in ji shi. Ya ce, ko da yake ana ci gaba da yin garkuwa da mutane a jihar amma bai yi muni kamar yadda ake yi a baya ba.