✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harkar fim da dadi da wuya – Khalifa Bello

An haifi jarumi Khalifa Bello BB a garin Gusau da ke Jihar Zamfara. Ya yi bayanin yadda ya fara harkar fim, inda ya ce harkar…

An haifi jarumi Khalifa Bello BB a garin Gusau da ke Jihar Zamfara. Ya yi bayanin yadda ya fara harkar fim, inda ya ce harkar tana kunshe da dadi da kuma wuya

Yadda na fara harkar fim
Tun ina karami nake matukar sha’awar kallon fina-finan Indiya, zan iya tunawa akwai wani kawuna Allah Ya jikansa shi ke fassara mana yarensu idan muna kallo, wasa-wasa saboda kallo yau da kullum har na iya yaren, har ya zama wani lokaci idan ina kallon sai na ji kamar da ni ake yi, tun daga nan ne na fara mafarkin in zama dan fim.
Bayan na sanar da kawuna sai ya fada wa mahaifiyata burina, inda suka rika yi mini dariya. Ko mahaifina ma bayan an fada masa sai ya rika dariya. Daga baya suka fahimci da gaske nake, sai kawuna ya hada ni da Ali Nuhu da sauran ‘yan fim, da haka na zama dan fim inda na fara da fim din ‘Malika’.
Fina-finan da na yi
Fina-finan da na fito a ciki sun hada da ‘Malika’ da ‘Zare Da Abawa’ da ‘Ke Duniya’ da ‘Ahlil Kitabi’ da ‘Matawalle’ da ‘Cikar Buri’ da ‘Tsananin Rabo’ da ‘Sirri Ne’ da ‘Kudi A Duhu’ da ‘Jarumin Maza’ da ‘Matar Hamza da ‘Ni Da Ke Mun Dace’ da ‘Nas’ da ‘Zawarawa’ da sauransu.
Rol din ‘dan Beauty’ a fim din ‘Zawarawa’
A lokacin da furodusan fim din Abdul’Azid dan Small ya kira ni cewa ina cikin fim din na ji dadi. Bayan na karanta labarin ne sai na ga ban taba fitowa a babban rol a fim kamar wannan ba, ko lokacin da muke daukar fim din kunnena ya ji maganganu iri-iri. A wurin mata da maza sai zolaya ta suke yi da ‘dan Beauty’, idan ana kira na da sunan sai in rika jin kunya ta kama ni saboda sunan ya fi cancanta da mace kyakkyawa ne.
Burina
Babban burina in zama jarumi kamar Ali Nuhu.
kalubale
Kalubalen da nake fuskanta ko kuma in ce muke fuskanta bai wuce yadda masu kallo ke yi mana ba, a fim ne za ka fito a wani rol sai a rika kallon ka da abin, ka ga ai babu fahimta a nan. Bari in ba ka misalin abin da ya faru da ni, akwai wata mai son fina-finan Adam A. Zango da ta samu lambata, sai ta rika turo mini sakonnin bakaken maganganu duk a dalilin abin da na yi masa a fim din ‘Ni Da Ke Mun Dace’, kasancewar a fim din  na tsane shi, ka ga a nan ba ta fahimta ba, ta manta cewa fim ne. Harkar fim da dadi da kuma wuya. Ya kamata mutane su rika fatimtar abin da suke kallo.