✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Horo kan zama lafiya ne mafi a’ala a lokacin Kirsimeti’

Mabiya addinin Kirista sun gudanar da bukukuwan Kirsimeti lafiya a Jihar Bauchi tare da yin kira ga daukacin Kirista su zauna lafiya da juna da…

Mabiya addinin Kirista sun gudanar da bukukuwan Kirsimeti lafiya a Jihar Bauchi tare da yin kira ga daukacin Kirista su zauna lafiya da juna da wadanda suke tare da su.

A bikin na bana mabiya addinin Kiristan sun samu tallafin kayan abinci da sutura daga manyan ’yan siyasa da  matar Gwamnan Jihar Bauchi, kuma a daya gefen su  ma sun rarraba kyaututtuka ga ’yan uwa da abokai har da wadanda suke tsare a kurkukun Bauchi.

Da yake gabatar da hudubarsa ta ranar Kirsimeti, Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Karamar Hukumar Bauchi, kuma  Shugaban Cocin ECWA na Daya da ke Rafin Zurfi a karamar hukumar, Rabaran Samaila Boro ya gargadi mabiya addinin Kirista su guji sayen kuri’a ko aikata magudin zabe a lokacin zabubbukan da ke tafe.

Rabaran Samaila ya ce kungiyar za ta fadakar da mabiya kan guje wa aikata duk wani abin da zai kai su ga karya dokokin zabe a lokacin zabe mai zuwa, sannan ya shawarce su da su yi amfani da bikin Kirsimetin domin nuna kauna da kyautata dangantaka da makwabtansu da kuma al’ummar da suke zaune tare da su sannan su taimaka wa marasa karfi.

A nasa hudubar, Rabaran Ejah Simon na Cocin  Busharar Kirista na ECWA da ke Kagadama ya hori Kiristoci su guji yin duk wani abu da zai kawo tashin hankali gabanin zabe mai zuwa da kuma bayansa.

Rabaran Simon ya bukaci su kasance jakadun zaman lafiya masu bin doka da gudanar da ayyukan da za su kawo dauwamammiyar lumana da kyautata tsaro cikin al’umma.

A Cocin Katolika da ke Bauchi kuma, kyautar rago da kayayyakin abinci suka rarraba wa wadanda ke tsare a gidan Kurkukun Bauchi ba tare da la’akari da bambancin addini ba. Da yake jawabi a wajen ba da kyautar, Limamin Cocin, Rabaran Hilary Dachelem ya ce wannan kyauta bangare ne daga cikin bukukuwan Kirsimeti,

Ya ce saboda haka ne ma suke taimaka wa kowa ba tare da la’akari da addinin da yake bi ba, da nufin ganin an samu fahimtar juna da kulla kyakkyawar dangantaka da tausayawa a tsakanin al’umma, sannan ya ce za su ci gaba da tainmaka wa wadanda suke tsare a gidajen yarin har sai sun zama mutane nagari.

Limamin ya shawarci wadanda ke tsare su rika zama lafiya da juna a gidan tare da la’akari da cewa zama lafiya abu ne mai muhimmanci wajen gina kasa, sannan ya shawarce su da yin amfani da kakyayyakin da aka sanya mu su a gidan don kyautata rayuwarsu sannan su mai da hankali wajen koyon sana’o’in da ake koya musu.

Da yake mai da jawabi, Mataimakin Kwanturolan Gidan Yarin, Suleiman Ibrahim Shanono ya gode wa limamin saboda wannan karamci, sannan ya roki sauran kungiyoyin addini su yi koyi da su.

Shanono ya roki jama’a su rika amfani da kayayyakin da mazauna gidajen yarin ke samarwa don taimaka musu su samu riba.

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Bauchi ta ce  ’yan sanda 2,832 ne za su kula da rayuka da dukiyoyin jama’a lokacin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara, inji Kakakin Rundunar, DSP Kamal Datti Abubakar.

Ya ce rundunar ta tsara yadda za a kula da majami’u da wuraren da za a gudanar da bukukuwa a cikinsu, ta tur tura jami’ansu domin bayar da kariya ga masu bukukuwan.

Abubakar ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi ya umarci dukan manyan jami’an ’yan sandan yankuna da sauran manyan masu kula da sassa su tabbatar da yin sintiri don gane wa idonsu ayyukan jami’an domin tabbatar da tsaro.

Ya gargadi masu yunkurin tada zaune tsaye a lokacin bikin Kirsimeti da sabuwar shekara cewa su sauya niyyarsu domin kuwa rundunar ba za ta bar su ba. Sai ya ba da layin waya na kar-ta-kwana don gaggauta sanar da su dukan wani abu da ke shirin haddasa tashin hankali kamar haka: 08151849417.