✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar zabe (INEC) za ta iya gudanar da zabubbuka a rana guda

A ’yan kwanakin nan ne Majalisar Dattijai ta fara yunkurin gyaran-fuska ga wasu sassan dokokin zabe, a yayin da ake tunkarar zabubbukan badi. Sanatocin sun…

A ’yan kwanakin nan ne Majalisar Dattijai ta fara yunkurin gyaran-fuska ga wasu sassan dokokin zabe, a yayin da ake tunkarar zabubbukan badi. Sanatocin sun bijiro da kudurori uku ne domin cin ma kwaskwarimar, duk da cewa ra’ayoin wasu daga cikinsu sun bambanta. Wasu daga cikin kudurorin sun hada da yiwuwar ba Hukumar Zabe ’yancin amfani da na’ura domin kidaya kuri’u a zabukan da za a gudanar nan gaba. Haka kuma akwai batun cire wa shugaban hukumar ikon nada Sakataren Hukumar, a mika shi ga Shugaban kasa, wanda haka zai kara wa kwamishinan zimma da nauyin daukar alhakin gudanar da aikinsa kamar yadda ya kamata, ba tare da katsalandan ba.
Sai kuma kudurin da ke kokarin ganin cewa hukumar zaben ta gudanar da zabubbuka dukkansu a rana daya. Kamar yadda Sanata Abu Ibrahim ya bayyana, yin haka shi ne tsarin da ya dace kuma shi ake yayi a kowane lungu na duniyar nan, ga shi kuma yana da saukin gudanarwa da kuma araha.
Sai dai abin takaici ne da aka ji Shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega a Litinin da ta gabata yana cewa ba zai yiwu hukumar ta gabatar da zabubbukan 2015 duka a rana daya ba. Duk da haka, abu ne mai kyau a shirya wannan tsarin, ko da ba a yi amfani da shi a zabubbukan badi ba, za a iya yi a can gaba.
Mu dai a ra’ayinmu, madamar ana son gudanar da ingantacce kuma amsasshen zabe a kasar nan, to kuwa a gudanar da shi a rana daya shi ne fa’ida. Lokaci ya yi da ya kamata a rage barnata dukiyar al’umma domin gudanar da zabe, don haka idan aka gudanar da zabubbuka duka a rana daya, babu shakka barnar za ta ragu. A lokacin da Sanata Abu ke fayyace fa’idar zaben rana daya, ya bayar da misalin yadda aka gudanar da zaben 2011, wanda aka yi ta jan kafa har ya kwashe kusan makonni uku, inda INEC ta biya ma’aikatanta na wucin-gadi Naira biliyan 50.
Wata fa’ida da za a kara samu idan aka yi zabubbuka a rana daya ita ce, za a samu shigar jam’iyyu masu yawa a zaben. Koda kuwa wasu jam’iyyun ba su kai karfin dukiyar jam’iyya mai mulki ba, za dai su samu sukunin shiga cikin tsarin zaben ba tare da wahala ba.
Haka kuma, gudanar da zabubbukan a rana daya zai rage matsalolin da ake fuskanta a zabukan da aka tsara a ranaku daban-daban, inda ake samun gane abin da zai faru a zabe na gaba, wanda haka kan sa masu zabe su. Abin bai zo da mamaki ba, yadda ’yan jam’iyya mai mulki suka nuna adawa da sabon tsarin gudanar da zaben da ake son dabbakawa. Shi kansa Shugaban Majalisar Dattijai, Dabid Mark ya kalubalanci tsarin, inda shi kuma Sanata Abdul Ningi ya tsaya kai da fata cewa majalisa ce ya dace kuma ta fi cancanta ta fitar da tsarin da ya kamata a gudanar da zabubbukan, amma ba INEC ba. Mu a ganinmu, wadannan gardandamin duk ba su kamata ba, domin za su kawo cikas ne kawai. Abin akwai mamaki da ake ta tada jijiyar wuya domin lalata kuduri ko tsarin da zai iya magance matsalolin zabe a kasar nan.
Wani abin lura ma shi ne, irin wadannan gardandami da tirjiya, ana dora su ne bisa son rai. Domin kuwa idan har INEC za ta iya gudanar da zabubbuka cikin kwanaki biyar, to me zai hana ta iya gudanar da su a rana daya kuma nawa take bukata domin yin haka? Idan an lura yawan mazabun da ake da su ba fa canzawa za su yi ba, don an ce za a yi zaben a rana daya. Don haka muna ganin cewa lallai gudanar da zabubbuka duka a rana daya shi ne mafi a’ala.
Daga yadda tarihi ya nuna kuma ya tabbatar, tsittsinka zabe zuwa ranaku daban-daban yana wahalarwa kuma yana tatse dukiyar kasa, musamman ma wajen biyan dauni ga ma’aikatan zaben da masu taya su, kamar jami’an ’yan sanda da na SSS da na dogarawan hanya da na sojoji da sauran hukumomi da ke da ruwa da tsaki wajen tallafa wa zaben. Babu shakka ya kamata a dauki tsari mai kyau, mai saukin gudanarwa kuma mai araha, wato na gudanar da zabubbka duka a rana daya.