✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Human Rights Watch ta bukaci Ajantina ta kama bin Salman

Kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Human Rights Watch, ta bukaci Gwamnatin Ajantina ta yi amfani da damar da tsarin mulkinta ya bayar, wajen kama…

Kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Human Rights Watch, ta bukaci Gwamnatin Ajantina ta yi amfani da damar da tsarin mulkinta ya bayar, wajen kama Yerima Muhammad bin Salman na Saudiyya kan zarginsa da hannu a kisan dan jaridar kasar, Jamal Kashoggi da kuma aikata laifuffukan yaki a Yemen.

Babbar Darakatar Kungiyar mai kula da yankin Gabas ta Tsakiya da kuma Arewacin Afirka, Sarah Leah Whitson ta ce sun dauki matakin mika bukatar ga Gwamnatin Ajantina ce, bisa la’akari da cewa Yerima Muhammad bin Salman zai halarci taron Kungiyar Kasashen G20 a wannan mako da zai gudana a Buenos Aires, babban birnin Ajantina.

Tsarin mulkin Ajantina ya bai wa hukumomin tsaron kasar damar kama duk wanda ake zargi da aikata laifuffukan yaki da suka hada da azabtarwa da kisan gilla, domin bincikarsa ba tare da la’akari da inda aka aikata laifuffukan ba.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, Babban Alkalin Ajantina, Ariel Lijo da ofishin babban mai gabatar da kara ba su ce komai ba game da bukatar Human Rights Watch duk da cewa sun karbi kiran a rubuce.

Kisan gillar da aka yi wa dan jarida Jamal Kashoggi a ofishin jakadancin Saudiyya da ke Turkiyya mako 6 da suka gabata, ya raunana dangantakar Saudiyya da kasashen duniya da dama, kazalika ya rage kimar Yarima mai jiran gadon sauratar kasar ta Saudiyya, Yarima Muhammad Bin Salman.