✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Idan ajali ya yi kira, ko babu ciwo sai an je

Barka da warhaka Manyan Gobe Yaya karatu? Ina fata kuna cikin koshin lafiya.A wannan makon Kawunku Bashir Musa Liman ne ya yi muku guzurin labarin…

Barka da warhaka Manyan Gobe

Yaya karatu? Ina fata kuna cikin koshin lafiya.
A wannan makon Kawunku Bashir Musa Liman ne ya yi muku guzurin labarin ‘Idan ajali ya yi kira ko babu ciwo sai an je’. Ina fata za ku bi labarin sau da kafa don ku kalaci darussan labarin.
A sha karatu lafiya.
Taku: Gwaggwago Amina Abdullahi

Idan ajali ya yi kira, ko babu ciwo sai an je

Daga Bashir Musa Liman

Wani saurayi ne mutuwa ta same shi a gidansa, sai ta yi masa sallama, bayan ya amsa ne, sai ta ce sunanta mutuwa kuma ta zo daukar ransa. Cikinsa ya duri ruwa, sannan cikin rawar baki ya ce ta yi hakuri, sai ta ce, ai sunansa ne na farko don haka da shi za ta fara. Bayan ya yi gardama sai ta nuna masa sunayen, inda kuma ya ga shi ne na farko.  
Ana cikin haka ne sai dabara ta fado masa, sai ya ce: “Kafin ki dauki raina bari na kawo miki abinci ki ci, kin ga za ki fi jin dadin gudanar da aikinki.” Sai mutuwa ta amince.
Bayan ya zuba mata abincin ne sai ya hada da maganin barci, ai kuwa tana gama cin abincin sai barci ya kwashe ta.. Ganin ta yi barci sai ya mayar da sunansa karshe.
Ya rika murna a ganinsa dabararsa ta biya, bayan mutawa ta farka ne sai ta ce: “Tun da nake ba a taba yi mini abin alheri irin wannan ba, saboda haka zan fara da na karshe.”
Darasin labarin:
Babu mai ikon canza hukuncin Allah (SWT).