✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

IRI da USAID sun shirya gangamin sanar da mata tsarin shiga siyasa

A ci gaba da fuskantar zabukan 2019, Hukumar IRI tare da hadin gwiwar USAID sun bukaci mata da ’yan kungiyoyin siyasa da su san tsarin…

A ci gaba da fuskantar zabukan 2019, Hukumar IRI tare da hadin gwiwar USAID sun bukaci mata da ’yan kungiyoyin siyasa da su san tsarin da za su bi wajen zama gwaraza idan siyasa ta gabato.

Shugaban IRI na Najeriya, Mista Sentell Barnes ne ya bayyana hakan a taron da suka gabatar wadda mutum sama da dubu biyu suka halarta. Ya ce akwai kungiyoyin da aka share su a wajen siyasa wadda ba su san damarsu ba.

Ya kara da cewa a tsarin dokar kasar nan akwai inda aka ce nakassashe zai iya yin zabe kuma a zabe shi a matsayin shugaba, amma da yawa daga cikinsu ba su san hakan ba. Sentel ya nuna wata kwakkwarar hujja game da shirya wannan taron na cewa mata da dama ba su bin dokokin tsarin siyasa shi yasa ba su cika samin nasarar gudanar da zabe ba.

Ya ce dole ne IRI ta zo wajen ganawa da jihohi domin samin damar ganawa da wadanda ke bukatar taimakonsu, sannan ya yi nuni da cewa mata kashi 75 ne a kasar nan ke iya sanya a ci zabe ko kuma a fadi.

Kwamishinan Mata na Jahar Adamawa, Zubairu Tola ya ce Jahar Adamawa ta yi kokarin sanya mata a mukamai daban-daban sannan ya dauki alkawarin kara kwazo da hazaka wajen ganin mata sun shiga siyasa dumu-dumu.