✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iyalai 135,000 sun samu tallafin abinci a Katsina

Gwamnatin Katsina ta raba tallafin kayan abinci ga iyalai marasa karfi 135,000.

Gwamnatin Katsina ta raba tallafin kayan abinci ga iyalai marasa karfi 135,000 a  fadin Jihar.

Da yake bayani a taron rabon kayan tallafin karo na biyar, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Tasiu Musa Maigari, ya bukaci masu rabon da su yi tabbata kayan sun isa ga iyalan da suka cancanta.

Mataiminsa kuma Shugaban Kwamitin Rabon a yankin Funtua, Shehu Dalhatu Tafoki, ya ce iyalai 8,465 sun samu tallafin a yankin, sannan ya bukaci jama’a da su yawaita addu’o’i a wannan watan na Ramadan don samun tsaro da aminci.

A yankin Katsina inda iyalai 600 za su amfana kuma, an ware kayan tallafin da suka hada da masara, gero da dawa.

Da yake kaddamar da rabon yankin, Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Mannir Yakubu, ta hannun Alhaji Salisu Ado Shinkafi, ya ce an ba da tallafin ne domin saukaka wa iyalai masu karamin karfi halin da suke ci.

Ya kuma bukace su da su yi amfani da kayan da suka samu ta hanyar da ta dace.