✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jaka biyu zan bayar!

Akwai wani Bafulatani, wanda muna cikin mota za mu je Falgore sai ya tare mu, ya ce: “Falgore!” Aka ce ya hau. Bayan nan sai…

Akwai wani Bafulatani, wanda muna cikin mota za mu je Falgore sai ya tare mu, ya ce: “Falgore!” Aka ce ya hau. Bayan nan sai kwandasta ya ce: “Kawo kudinka.” Danfulani ya ce: “Nawa? Kwandasta ya ce: “Naira dari uku da hamsin.” Danfulani sai ya ce: “Wallahi ba zan ba da Naira dari uku da hamsin ba saboda yanzu na zo a jaka biyu, ta yaya za a kara kudin mota ko kwana ba a yi ba? Ni wallahi in ba jaka biyu ba a sauke ni.”

Daga Tahir Mamud Kano, 08100987777

 

Me ya hada ni da buje?

Wani Banufe ne yana fada da matarsa ranar wata Juma’a, sai makwabtansa suka zo domin sasanci. Ana kan sasanci har aka kai ga tayar da Sallah. Sai ya fisgo wani abu da hannunsa daga dakin matarsa, sannan ya fito daga gidan a fusace. Abin nan da ya dauko ya yi zaton darduma ce, ashe bai kula ba bujen matarsa ce ya dauko. Koda ya zo an yi raka’ar farko har an sunkuya ruku’i a raka’ar karshe. Koda ya shimfida ya duka sai ya ga ashe bujen matarsa ne ya dauko, sai ya kama fada yana cewa: “Me ya hada ni da buje?”

Daga Junaidu Dan Iliya Dangulbi, 08032342258

 

Yau talauci ya yi rana!

Wani Bafulatani ne ya je zai hau mota a tasha zuwa wani wuri, kudinsa ba su cika ba aka ki yi masa ragi, a nan aka bar shi a tasha. Mota ta tafi ba a yi nisa ba, sai ta yi hadari wadansu suka rasu, wadansu suka ji ciwo, sai aka dawo da su. Bafulatani ya ce: “Me ya faru? Sai aka fada masa cewa motar nan da ta tashi ne ta yi hadari. Bude bakinsa sai ya ce: “Aradu yau taulaci ya yi rana!”

 

Wane walakanci ne ban gani ba!

Wani tsoho ne ya zo wucewa a kan tsohon babur dinsa ta wurin duba ababen hawa na sojoji. Sai wani soja ya rika cewa “Wait, Wait Baba ka tsaya,” amma tsohon nan ya wuce bai tsaya ba. Can sai tsoho ya dawo, sojan nan ya tare shi, ya ce “Baba wallahi yau sai na yi maka wulakanci.”

Sai tsoho ya ce haba yaro shekarata 45 tare da mace daya wane irin wulakanci ne ban gani ba?

Labarai daga 09099886988

 

Shekarata 30 ina Sallah da ita

Wani yaro ne ya shiga ban-daki ya fara wakar “Dala’al Badru alaina, min saniyatil wada’i.” Sai mahaifinsa ya ji, kawai ya fito da shi daga ban-dakin ya hau dukarsa, yaro ya kama kuka. Sai mahaifiyar yaron ta tambaya me ya yi aka dake shi. Sai mahaifin ya ce “Na ji yana karanta Alkur’ani ne a ban-daki?” Sai ta ce wannan fa ba Alkur’ani ba ne waka ce sananniya.

Sai mahaifin ya koma gefe ya yi tagumi yana istigfari. Sai matar ta ce me ya faru? Sai ya ce “Wallahi shekarata 30 ke nan ina karanta ta a cikin Sallah!”

Daga 09092969381