✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jakadun Amurka da Turai sun kasa sasanta rikicin Masar – Fadar Shugaban kasa

kokarin kasashen da jami’an difulomasiyar Larabawa na sasanta rikicin siyasar da ya dabaibaye kasar Masar ya ci tura, a cewar shugaban kasar. An bayar da…

Magoya bayan shugaba Mursikokarin kasashen da jami’an difulomasiyar Larabawa na sasanta rikicin siyasar da ya dabaibaye kasar Masar ya ci tura, a cewar shugaban kasar. An bayar da wannan sanarwar ne daidia lokacin da Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen AMurka Willim Burns ya bar birnin Alkahira, inda ya kasa cimma matsaya a tsakanin gwamnatin da sojojin kasar suka akfa da magoya bayan Jam’iyyar Musulunci ta hambararren shugaban kasa Mursi.
“Yunkurin sasancin difulomasiya ya kare a yau,” a cewar fadar shugaban kasa, inda aka yi nuni da kokarin da Mista Burns da Jakadan Tarayyar Turai ta EU Bernardino Leon suka yi a birnin Alkahira.
“Wannan kokarin da aka yi bai haifar da sakamako mai kyau ba,” a cewar sakon da aka fitar.
Gwamnatin soja ta bai wa ’yan uwa Musulmi ministoci uku, a gwamnatin hadin gwiwa da ake shirin kafawa, sannan za a sako wasu daga cikin mutanensu dake kurkuku, kamar yadda wata majiya da ke kusa masu kokarin sasanta rikicin ta bayyana.
Gwamnati ta karyata, amma ta tabbatar da cewa akwai alkawuran da ta yi wa ’yan uwa Musulmi da zarar sun daina zaman dirshan din da suke yi don kawo karshen zanga-zanga,” a cewar majiyar jami’an tsaro, kamar yadda ta bayyana wa jaridar Guardian ta Birtaniya.