✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaro a Legas suna yawan kamun ’yan Arewa

Shugabannin ’yan Arewa mazauna Jihar Legas sun koka da yadda jami’an tsaro ke kamen ’yan Arewa mazauna jihar, wadanda ba su yi laifin komai ba,…

Shugabannin ’yan Arewa mazauna Jihar Legas sun koka da yadda jami’an tsaro ke kamen ’yan Arewa mazauna jihar, wadanda ba su yi laifin komai ba, ana alakanta su da kungiyar ’yan ta’addar Boko Haram.
A karshen makon jiya ne ’yan sandan yankin Unguwar Sabo Yaba suka kai samame wani gida da dare tsaka, suka tada mutanen da ke barci a gidan su kimanin 121, suka kame su da sunan ’yan Boko Haram ne.
Sarkin Hausawan Jihar Legas, Alhaji Sani Kabiru ya shaida wa Aminiya cewa mutanen da aka kama suna zaune a gidan, sama da shekaru 20. Mafi yawancinsu ’yan acaba ne da masu dakon lemu da sauran kananan sana’o’in da suke gudanarwa a yankin. “Akwai kungiyar Tambarin Arewa da suka dau lauya suka je wajen shugaban ’yan sandan yankin, suka tambaye shi dalilin kamen sai ya ce musu daga sama aka ba shi umarni.  Bayan labarin kamen ya riske mu sai na sanar wa Kwamishinan ’yan sanda. Ya shaida mana cewa zai bincika,” inji sarkin.
Ya shaida wa Aminiya cewa ba a kama wadanda ake zargin da ko wani makami ba kuma su ma majalisar sarakunan na kalubalantar hukuma saboda ire-iren kamen da ake wa jama’arta na ba gaira ba dalili, a kwace musu dukiyarsu sannan a ce ’yan Boko Haram ne.
Abdullahi Umar Kawoji, dan uwan mutanen da aka kama nae, ya shaida wa Aminiya cewa: “Mutanen ’yan karamar Hukumar Bagudu ne a Jihar Kebbi kuma suna yin sana’oinsu ne a yankin. Makwabtansu ’yan kabilar Ibo ne suka yi musu kazafin saboda ba su kaunar zaman su a wajen.