✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’in alhazai ya yi layar zana da Naira miliyan 30 na maniyyata

Wani jami’in Alhazai na karamar Hukumar Bosso a Jihar Neja, mai suna Alhaji Ahmad Bala Barkuta ya yi layar zana da sama da Naira miliyan…

Wani jami’in Alhazai na karamar Hukumar Bosso a Jihar Neja, mai suna Alhaji Ahmad Bala Barkuta ya yi layar zana da sama da Naira miliyan 30 na maniyyata aikin Hajjin bana da aka biya ta hannunsa.
Kakakin Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar, Malam Sani Awwal ne ya shaida wa Aminiya haka a ofishinsa, inda ya ce an gano badakalar ce lokacin da shirye-shirye suka yi nisa domin fara jigilar maniyyatan jihar fiye da dubu uku zuwa Saudiyya.
Malam Sani Awwal ya ce wanda ake zargin ba sabon hannu ba ne, ya shafe fiye da shekara shida ana aiki da shi ba tare da wata matsala ba, sai a wannan karon kuma ya san babban laifi ne mutum ya karbi kudi a hannun maniyyata aikin Hajji. “Abin da ya kamata ya yi, shi ne ya jagorance su zuwa banki domin su biya,” inji Kakakin.
Ya ce, su ma maniyyatan da suka biya kudin ta hannun Alhaji Ahmad Bala Barkuta suna da laifi, domin an sha gargadi a kafofin watsa labarai kan illolin da ke tare da yin haka. Ya ce lamarin ya tayar wa shugaba da ma’aikatan hukumar tasu hankali.
Malam Awwal ya ce an shiga neman jami’in don ya yi wa hukumar bayanin yadda ya yi da kudin. Kuma ya ce hukumar za ta yi nazarin abubuwan da suka dace a yi domin wadanda lamarin ya rutsa da su, su samu damar sauke farali a bana.
Shugaban Hukumar Mai shari’a Jibrin Ndatsu Ndajiwo ya ba da umarnin a kamo jami’in duk inda aka gan shi domin bincikarsa ka yadda ya yi da kudin.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa wai wasu mutane sun yi ta kiran Alhaji Ahmad Barkuta a waya suna yi masa barazanar cewa zai haukace muddin bai ba su kudin maniyyatan ba, shi kuma sai ya mika musu daga nan ya yi layar zana inda hatta lambobin wayarsa ba su aiki.