✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’in Kwastam ya yi wa kansa karin girma ya nemi jan ragamar Hukumar

Wani abu mai kamar wasan kwaikwayo ya faru a yau a babban ofishin Hukumar Kwastam ta kasa da ke Abuja inda wani jami’in Hukumar mai…

Wani abu mai kamar wasan kwaikwayo ya faru a yau a babban ofishin Hukumar Kwastam ta kasa da ke Abuja inda wani jami’in Hukumar mai anini biyu mai suna Nura Dalhatu Katsina. Ya yi wa kansa karin girma zuwa CGC wato mukamin shugaban rundunar ta kasa inda ya nufi ofishin shugaban rundunar Kanal Hamid Ali domin ya yi masa hand oba wato ya miqa masa ragamar Hukumar bayanai sun nuna cewa, tuni ‘yan sandan rundunar ta Kwastam suka kame jami’in.

Wakilin Aminiya ya tuntubi mai magana da yawun Hukumar ta Kwastam mukaddashin Kwanturala Joseph Attah, domin karin haske sai dai lambar wayar salular sa ba ta shiga kana bai bayar da amsar sakon da wakilinmu ya tura masa ba har izuwa lokacin hada wannan rahoton.